Yadda masu son muƙamin shugaban majalisar dattijai ke sayen ƙuri’un sanatoci – NdumeMajalisar dokokin Najeriya

A Najeriya bayan kammala zaɓukan ƙasar a yanzu hankali ya karkata kan shugabancin zaurukan majalisun dokoki.

Tuni dai wasu ‘yan majalisun da ke son ɗarewa kujerun shugabancin majalisun suka fara bayyana sha’awarsu ta hanyar kamun ƙafa a wajen masu ruwa da tsaki na jam’iyyunsu da kuma zaɓaɓɓun ‘yan majalisar.

Sai a watan Yuni mai zuwa ne za a ƙaddamar da majalisar dokokin ta goma, daga nan kuma a fara shirye-shiryen zaɓen shugabannin majalisun.

To sai dai wasu ‘yan majalisun sun fara zargin cewa ana amfani da kuɗi wajen sayen bakin ‘yan majalisun domin zaɓen wasu a matsayin shugabannin majalisun.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like