Yadda Muke Magance Matsalar Masu Zuwa Yi wa Kasa Hidima Da Takardun Kammala Karantu Na BogiSama da matasa dubu 90 ne hukumar NYSC mai kula da matasa masu yi wa ƙasa hidima a Najeriya ke kan samun horo a sansanoninta 36 hade da babban birinin tarayya Abuja a fadin kasar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta bude shirin horas da matasa wadanda suka kammala karatun jami’a daga ciki da wajen Najeriya a zango na biyu diba na farko na shekarar 2022.

A hirarsa da Muryar Amurka, sabon shugaban hukumar ta NYSC na 19 Birgediya Janar Mohammed Kaku Fada, ya ce hukumar ta dauki tsauraran matakan tsaro da za su kare matasan a dukkan jihohi 36 har da babban birnin tarrayar kasar Abuja wadanda za’a ba su horo na yi wa kasa hidima a wanna karon na makonni 3.

Wasu masu yi wa kasa hidima na NSYC a Najeriya

Wasu masu yi wa kasa hidima na NSYC a Najeriya

‘’Ina so na janyo hankalin duk wanda zai je horo na NYSC da ya kwantar da hankalinsa domin mun dauki dukkan matakan da su ka dace wajen tabbatar da an duba walwala da samar da tsaro ga masu yi wa kasa hidima a ko ina a fadin Najeriya’’ in ji Birgediya janar Kaku Fada.

Ko da yake shugaban ya tabbatar da cewa akwai wasu jihohi 3 da suka hada da Sokoto, Kebbi da Zamfara da aka jinkirta fara shirin baiwa matasan horo na makonnin 3 saboda matsalar tsaro amma nan da ‘yan kwanaki su ma za su fara nasu, domin kuwa an dauki matakan tsaron da suka dace don tabbatar cewa matasan sun karbi horo cikin tsaro da walwala.

Da yake jawabi kan matasan da ke dauke da shedar kammala karatunsu na bogi, shugaban ya ce za’a ci gaba da gudanar da jarrabawa ta musamman da hukumar ta NYSC ta saba da ke kula da aikin tantance masu aikata irin wannan mumunan dabi’ar.

Birgediya Janar Kaku Fada ya ce, ‘’wani tsari ne da wasu ba sa son a ci gaba da yin shi, domin so tari hukumar NYSC ta sha samun matasan da ba su iya rubuta sunansu ba ballantana su iya rubuta wasikar neman yi wa kasa hidima hakan yasa su ke kalubantar tsarin amma hukumar zata ci gaba da yin shi domin tantance wadannan matasan”.

Dalibai da suka kammala karatu a aikin yi wa kasa hidima na NYSC a Najeriya

Dalibai da suka kammala karatu a aikin yi wa kasa hidima na NYSC a Najeriya

A cewar Fada, an taba samun kusan mutane dubu 60 da su ka yi rijista don yi wa kasa hidima amma da suka ji za’a yi wata jarabawa mutun dubu biyu kawai suka fito daga cikinsu.

Birgediya Janar Kuka ya jadadda kudirinsa na aiwatar da ayyukan da hukumar ta sa a gaba inda ya ce zai ci gaba da ayyukan da wanda shi ya gaje shi wato aikin da Birgediya Janar Shu’aibu Ibrahim ya bari, inda ya ce akwai shirye shirye da ake da su wadanda za su inganta aikin hukumar.

A shekara mai zuwa ta 2023 ne ake sa ran hukumar za ta cika shekaru 50 da kafuwa wacce ke ci gaba da tsayawa kan dalilan da ya sa aka kirkirota tun farko wato hada kan ‘yan kasa.

A saurari cikakken bayani daga bakin shugaban hukumar NYSC cikin sauti:

You may also like