
Sannu a hankali mutane na gane irin alamomi da birrai ke amfani da su wajen tattaunawa tsakaninsu.
Wannan na kunshe ne cikin wani hoton bidiyo da aka gudanar da bincike, inda ‘yan sa kai suka yi kokarin sanin irin alamomin. Jami’ar St Andrews ce ta gudanar da binciken.
Binciken ya nuna cewa dangin birrai na karshe da suka rage, su ma suna amfani da waɗannan alamomin, inda hakan ya nuna mafara ga harshen mu.
An wallafa binciken da aka gudanar a mujallar the scientific journal PLOS Biology.
Shugabar binciken, Dakta Kirsty Graham daga Jami’ar St Andrews ta ce kashi 95 na dukkanin dangogin birrai na amfani da irin waɗannan alamomi ko kuma salon magana wajen tattaunawa tsakaninsu.
“Don haka muna da shakkar cewa wanann wani abu ne da dangin birrai na karshe ke da shi. Amma muna da ƙwarin gwiwa tun da yanzu birran suna amfani da alamomi wajen yin magana.’’
Wannan bincike na cikin koƙari da bangaren kimiyya ke yi na gane asalin tushen wannan harshe ta hanyar yin ƙwakkwaran bincike na yadda birrai da ‘yan uwansu ke magana.
Tawagar masu binciken sun shafe tsawon shekaru suna yin bincike kan birrai. A baya, sun gano cewa manyan birrai na amfani da alamomi kusan 80 kowanne kuma da irin na shi sakon zuwa ga wani dangi na ‘yan uwansu.
Suna amfani da salo daban-daban wajen yin magana kamar taɓa baki na nufin ‘a bani abinci’ sanna cire ganye daga kan itatuwa da hakori, salo ne na nuna soyayya.
Masana kimiyya sun yi amfani da gwaje-gwajen sake kunna bidiyo, saboda an yi amfani da tsarin gargajiya don gwada fahimtar harshe a cikin abubuwan da ba na ɗan adam ba.
A cikin wannan binciken, sun karkatar da tsarin don tantance iyawar ɗan adam don fahimtar yanayin dangin birrai na kusa.
Masu sa kai sun kalli bidiyo na alamomin birrai, sannan aka zaɓa daga jerin fassarori da yawa.
Mahalarta taron sun yi matukar kokari fiye da yadda ake tsammani, suna fassara daidai ma’anar birrai da kuma motsin su sama da kashi 50.
“Mun yi mamakin sakamakon,” in ji Dakta Catherine Hobaiter daga Jami’ar St Andrews. “Ya bayyana cewa dukkanmu za mu iya yin shi, wanda yake da ban sha’awa na sadarwa kuma yana da matukar ban haushi a matsayin masanin kimiyya wanda ya kwashe shekaru yana horar da yadda ake yin shi,” in ji ta.
Alamomin da mutane za su iya fahimta da gaske na iya zama wani ɓangare na abin da Dakta Graham ya bayyana a matsayin “tsohuwar abin halitta na ƙamus ɗin da aka raba tsakanin manyan nau’in birrrai ciki har da mu”.