
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya sun ce mutum biyar ne suka mutu a lokacin da suke tsaka da bikin murnar shiga sabuwar shekara a jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Adewale Osifeso ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a lokacin da wasu matasan ke gudanar da bikin murnar shiga sabuwar shekara a garin Akinmorin da ke yankin ƙaramar hukumar Afijo da ke jihar.
Mista Osifeso ya ƙara da cewa matasan na tsaka da gudanar da bikin ne a daidai lokacin da hatsaniya ta kaure tsakaninsu a lokacin da ɗaya daga cikinsu ya tuƙo mota tare da kutsowa wajen da suke gudanar da bikin.
Abokan sun yi ƙorafin yadda mutumin ya kutso cikin harabar bikin
Mutumin ya ce bai ji daɗin yadda abokanan nasa suka yi masa ba, daga baya ne kuma gardama ta kaure tsakaninsu
“Manya sun shiga tsakani tare da kwantar da hankula, to amma lamarin bai yi wa wanda ya tuƙo motar daɗi ba, ya yin da ya yi zargin cewa sun bashi laifi.” kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana
“Dalilin kenan da ya sa ya koma cikin motarsa tare da ikirarin cewa sai ya zubar da jinin wasu, daga nan kuma sai ya tuƙa motar tasa tare da take abokan gardamar tasa har ma da wasu mutanen daban kamar 10 waɗanda ke tsaka da rawa.
”Daga nan kuma sai ya fice daga motar tare da guduwa daga wajen da ake gabatar da bikin” in ji ‘yan sanda.
Haka kuma ‘yan sandan sun ce sun kama mutum uku daga cikin abokansa waɗanda suka zo tare cikin motar.
Mista Osifeso ya ce hukumar ‘yan sanda na bincike game da lamarin, kuma da zarar sun kammala binciken to za su fitar wa da jama’a sanarwa