Abdurraheem ya rubuta wani kundin wakoki da yake kira ‘Etterath’.
Abdurraheem Koko dalibi mai shekara 17 ne da ke karatu a Jami’ar Nile da ke Abuja.
Mahaifin Abdurraheem – wanda shi da dan uwansa sun kasance tagwaye – ya mutu tun suna da shekara daya da haihuwa.
Sai dai duk da bai san mahaifinsa ba yayin da yake tasowa, marubucin wakokin ya dade yana kewar mutumin da bai taba gani ko sani ba a rayuwarsa.
Sai dai a maimakon ya rika koka wa da halin da ya sami kansa, sai ya rika rubuta dukkan abin da ya rika zo masa a matsayin baitukan wakoki.
Wannan ne ya zama hanyar zamansa fasihi har ya zama abin da ake kira ‘likitan wakoki’.
A halin yanzu, Abdurraheem ya rubuta wani kundin wakokin da ya lakaba musu sunan ‘Etterath’.
Ga mawakin yana ba masu sha’awar zama marubuta shawarwarin yadda ake rubutun wakoki.