Yadda Na Karbi Tsurar Kudi Dala Miliyan 4 Daga Fadar Gwamnati – Shaida


 

 

 

Wani mai bayarda shaida a kotu a karar da EFCC ta shigar da tsohon mai taimakawa tsohon shugaban kasa Gooodluck Jonathan Waripimo Dudafa, ya bayyanawa kotun yadda ya karbi dala miliyan 4 tsurarsu (wadanda suka yi dai-dai da naira biliyan 1.6) daga hannun wanda ake karar a fadar gwamnatin tarayya.

Mai bayarda shaidan, Murtala Abubakar wanda dan canji ne ya adar da cewa ya karbi kudade ne da daga hannun Dudafa da sunan kamfanoni 5 da suka hada da – Pluto Properties and Investment Limited, Avalon Global Property, Rotato Interlink Services, Seagate Property da kuma Ebiwise Services Limited – tsakanin shekarar  2013 da 2015.

Hukumar EFCC dai na tuhumar Dudafa da wani Joseph Iwejuo da laifukan 23 da suka hada da sakile laifuka, rike kudaden sata, da kuma kin samar da bayanai ga jami’an tsaro kuma ta shigar da kara a gaban alkali Mohammad Idris na katun gwamnatin tarayya da ke jahar Lagos.

Abubakar ya kuma bayyanawa kotun cewa ya san Dudafa tun lokacin da yake kwamishinan kananan hukumomi a jahar Bayelsa kuma alakar da ke tsakanisu ta kasuwancin canji ce kawai wacce ta ci gaba ko bayan da ya zama mai taimakawa shugaban kasa na musamman.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like