
Asalin hoton, Maher Mezahi
A wani yankin da ke gefen Skikda da ke birnin Maditerran na Algeria, wanda ya yi iyaka da tashar jirgin ruwa, dangina na da wani fili a wajen.
A wajen mahifiyata da ‘yan uwanta, filin ya zama wajen wani shaƙatawarsu da suke zuwa, idan unguwar da suke zaune mai cunkoson jama’a ta yi musu zafi.
A lokacin zafi sukan tattara su tafi wajen da kayan shaye-shayensu, su ci su sha, su yi wasanni da ‘yan uwanta.
A wajena da yan uwana, ziyarar wurin yana nufin, za mu yini cur ba tare da samun sabis na waya ba, ba za kuma na ga korayen tsirran da ke gefen gonata ba ta kwakwar manja.
Ba wani ja, dukkanmu muna ɗaukar filin mai matuƙar muhimmanci, saboda yadda yake a kan wani kwari da ya gangara.
Wata hanya mara kyau da ke kai mutum saman tudu, inda nan ne maƙabartar da ‘yan uwanmu ke kwance da yawa cikin nutsuwa.
Babu hayaniyar komai sai ta kaɗawar ganyen bishiyar turare.
Babu wata ziyara da muke zuwa yankin Skikda sai mun fara kai ziyara ga maganatanmu da suka riga mu gidan gaskiya.
Duka mutanen da nake girmamawa matuƙa na kwance ne a wannan tsaunin, ciki har da kakannina na wajen uwa da na uba.
Bayan ziyararsu da nake yi, sai in shiga neman kakanin kakannina, Ahmed.
Wani ƙarfe mai kauri da ke da fenti kore shi aka sa a matsayin alamar cewa an haife shi a shekarar 1845.
Kullum abin yana taɓa zuciyata in na tuna waɗannan ne asalin tarihina.
Asalin hoton, Maher Mezahi
Ba abu bane da aka saba a ƙasata ko kuma nahiyar da na fito mutum ya san iyayen iyayensa na ƙarni huɗu, kuma nan da nan na fahimci irin ƙimar da nake da ita.
A lokacinsu babu yadda ake ƙidaya ko shaidar mutuwa, mafi yawanmu da baki ake faɗa mana kakanin kakanninmu.
A dukka faɗin al’adar Afrika wani abun ƙimane sanin dangin da ka fito ta tsatsnsu, sau da dama samun bayanansu abu ne mai wuya.
A kwanan nan, na riƙa tuntuɓa da wayata da kuma abokaina domin ganin yadda suka riƙa sanin iyayensu.
Abokan aikina da ke Ghana da Afrika Ta Kudu sun tabbatar min da cewa sun san ‘yan uwansu ne kawai ta yadda ake basu labari da baki – kawunnansu ne ke basu labari da ‘yan uwan iyayensu, za su iya bibiyar kakanin nasu amma ba sa wuce kaka na uku.
An bar mata a baya
Wani abokina a Habasha ya faɗa mani cewa a ƙasarsu “wajibi ake yiwa yara su haddace zuri’arsu.”
Sai dai tsarin yadda suke haddace sunayen ya tsakaita ne kan iyayen maza da kuma kakanninsu maza kawai.
Wani abokin nawa a Masar ya shaida mani cewa a ƙasarsu haka ake kiran yara da sunayen iyayensu da na kakanninsu.
Irin wannan dabarun za su iya zama taƙaitattu ganin yadda ake amfani da su wajen riƙe sunayen mazan dangi kawai, wanda hakan ke nufin cikin sauƙi ake manta matan dangi kan maza.
A wasu lokutan ina begen samun dumbun bayanai kan yawan jama’a a wasu sassan duniya.
A Faransa misali, gwamnati na dora bayan aure da haihuwa da na mutuwa wanda kowa zai iya samu a shafinta na intanet.
A Ingila da Wales akwai bayanai kan duka haihuwar da aka yi da aure da kuma mutuwa tun daga 1837.
Sai dai a nahiyar Afrika muna da sauran tafiya kan mu fara ɗora namu bayanan a intanen domin amfanin kowa
Mene abun damuwa a kai?
Akwai wata magana da ake cewa “Idan baka san inda ka fito ba, bai zama dole kasan inda zaka je ba”.
Na riƙa yi wa kaina tambayoyi irin waɗannan watannin da suka gabata.
Daya daga cikin ribar sanin wannan tarihin na kanka shi ne zaka ƙara sanin kanka sosai.
Bayanan da za ka samu za su baka damar sanin asalinka da magungunan da za su iya yin daidai da jikinka.
Ni yanzu fatan da nake matasa su san cewa sanin asali a al’adance abu ne mai kyau.
Mafi mahimmanci a abubuwan da na koya shi ne, sanin asalin inda na fito.
Ba maganar tutar ƙasa ba ne, ko wani tunani. Maimakon haka, Ina ganin komawa ta Skikda inda salin iyayena suk shi mafi dadi a wannan lamari.
Komawa ta wajen bishiyar turare da yadda ta samar da tsatsaon kakannina shi ma ya yi min dadi, in ji Ahmad.