Yadda Najeriya Ta Yi Sanadiyyar Rugurgujewar Kamfanonin Shinkafa A Thailand


Matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na hana shigo da shinkafa daga kasar waje ya yi sanadiyyar rugujewar wasu manyan kamfanonin sarrafa shinkafa har guda bakwai a kasar Thailand.

Da yake tsokaci kan wannan batu, Ministan Gona, Audu Ogbe ya ce, a makon da ya gabata ne Jakadan kasar Thailand ya kai masa ziyara a ofis inda ya koka kan cewa rashin aikin yi ya karu da kashi hudu a kasarsa sakamakon rufe wadannan kamfanonin shinkafar wanda a can baya sune kan gaba wajen shigo da shinkafa cikin Nijeriya.

You may also like