
Asalin hoton, OTHER
‘Yan kasuwa da sauran al’ummar Najeriya na kokawa da matsalar rashin kyakkyawar sadarwar intanet abin da suka ce na kawo cikas wajen biya da kuma tura kudi musamman idan an yi sayayya.
Duk da shige da ficen jama’a a kasuwanni, ‘yan kasuwar sun ce hada-hada ta ja baya sosai, sakamakon karancin kudi a hannun jama’a da kuma wahalar da ake sha wajen tura kudi idan an sayi kaya.
BBC ta yi tattaki zuwa wasu kasuwanni jihar Kano, kasancewar cibiya ce ta kasuwanci a Najeriya kuma har daga kasashe makwabta ana zuwa cinikayya jihar.
Wani dan kasuwa Salihu Ibrahim Darma, ya shaida wa BBC cewa, tuni wasu suka fara hakura da bude shaguna saboda idan mutum ma ya je kasuwa sai ya shafe wuni guda babu masu siyayya.
Ya ce ,“ Ba-ba-ba, ta yi yawa a kasuwa, ga rashin kyakkyawar sadarwar intanet abin da ke kara jefa harkokin kasuwanci cikin mawuyacin yanayi“.
Shi kuwa Alhaji Idris Yusuf Muhammad, cewa ya yi dama can sun dade da wannan matsalar ta rashin kyawun intanet.
Ya ce,“ Dama tun kafin a shiga wannan yanayi na karancin tsabar kudi, mun yi korafin cewar muna samun matsala wajen tura kudi, sai mun sha wuya kafin ka tura kudi ko a tura maka ka samu a dukkan kasuwanninmu.“
Wannan matsala dai ga alama tana ciwa ‘yan kasuwa da dama tuwo a kwarya.
Alhaji Tijjani Ladan, ya shaida wa BBC cewa wani lokacin suna ji suna gani ciniki ma suke barinsa.
Ya ce.“ Babu ciniki kudi hannu, sau da dama sai azo a yi maka cinikin kaya mai yawa idan an tura maka kudi sai ka shafe sa’oi baka gansu sun shiga cikin asusun ajiyarka na banki ba, to wannan ne ya ke hanamu bayar da kaya, saboda ba zaka dauki kaya ka bawa mutumin da ka sani ba ya tura maka kudi kuma ka shafe kwanaki baka gansu ba, a ina zaka nemo shi?.“
Dan kasuwar ya ce, wani lokaci ma ida an tura maka kudi shi wanda ya tura sai ya ga an cire masa amma kuma kai baka gansu ba, sannan sai bayan wasu sa’oi kuma sai ya ga an mayar masa da su.
Ya ce don haka a yanzu kasuwanci ma a zaune suke babu shi.
Suma ‘yan kasuwar Singa da ke Kanon, sun koka da irin wannan matsalar, inda a yanzu hada-hada ta tsaya cak, domin baki masu sayen kaya basa zuwa, sannan su ‘yan kasuwar tsoro suke su bayar da kaya saboda kada a samu akasi wajen tura kudi asusun ajiya na banki.
Tuni dai shugabannin ‘yan kasuwar suka shaida wa BBC cewa a yanzu suna kokarin ganawa da hukumomi ko za a samu mafita.
Bayanai dai na cewa kasuwannin Kantin Kwari da Kofar Wambai da Galadima da Dawanau da kasuwar ‘Ƴan Kaba da kuma Kofar Ruwa, suma cinikin ya ja baya, baya ga matsalar karancin kudin ga kuma tsadar man fetur abin da ke sanya wasu ‘yan kasuwar basa zuwa hada-hada birnin na Kano sosai.