
Asalin hoton, Ghazal Farkhari
Kalmar ‘‘mano morta’’ na nufin ‘matacciyar hannu’’ a yaren Italiya. Iyaye mata da ‘ya’yansu mata sun sha tattaunawa kan batun, yayin da abokanai kuma ke korafi kan kalmar a tataunawar su ta yau da kullum, inda ake gargadin ‘yan mata da su yi taka tsan-tsan yayin zuwa makaranta.
Sai dai kalmar ta mataccen hannu ba labari ne kawai ba. Wani sabon salo ne da ake amfani wajen cin zarafin mata – inda kuma yake nuna yadda ɗimbin mata ke fuskantar cin zarafi na wasu sassa na jikinsu a tashoshin mota da na jiragen kasa.
A tsakanin ‘yan Italiya, kalmar tana nuna wannan mummunar dabi’a. Yawancin mata a fadin duniya sun fuskanci irin wannan cin zarafi, amma basu da wata kalma ta yadda za su fadi hakan a yarukansu.
A harshen Ingilishi, ana ci gaba da amfani da wasu kalmomi da ake kwatanta wa da cin zarafi kamar su ‘‘gaslighting’’ da ke nufin takurawa mutane ta yadda suke ganin abubuwa a zahiri da ‘‘upskirting’’ mai nufin daukar hoton mutum daga kasan kayan da mutum ya saka da ‘‘love bombing’’ da ke nufin turawa wani kyautuka masu tsada domin juya akalarsa.
Ana kuma yawan amfani da wadannan kalomomi wanda kuma ke cikin kamusun ingilishi na 2022, inda aka nemi sanin kalmar har sau 1,740 a shafin intanet a wannan shekara.
A shafin TikTok, mutane kusan biliyan 2 ne suka duba batun kalmar gaslighting yayin da kalmar lovebombing kuma mutum kusan miliyan 250.
“Idan muka duba lokacin da aka fara amfani da wadannan kalmomi domin kwatanta yadda mata ke fuskantar cin zarafi, lokaci ne gangamin kwato ‘yancin mata ta fara karbuwa,’’ a cewar Dr Alessia Tranchese, wani mai bincike kan yadda za a ci zarafin mata ta wadannan kalmomi.
Wani babban malami a sashin sadarwa da harsuna a jami’ar Portsmouth, Dr Tranchese, ya yi bincike kan yadda kalmomin ke bayyana cin zarafi a matsayin hanya ta kalubalantar jinsi.
“Za mu iya cewa harsuna na nuna yadda dangantaka take tsakanin maza da mata, kuma wuri ne da ake dabbakawa ko kuma sake kirkiro da shi,’’ in ji Dr Alessia.
Shin kirkiro da sabbin kalmomin zai iya taimakawa wajen dakile cin zarafi da mata ke fuskanta a fadin duniya?
Shirin BBC na mata mai suna BBC 100 Women, ya tattauna da wasu mata uku da ke yaɗa kalmar – musamman kan kwatanta cin zarafi – a Birtaniya da Kudancin Amurka da kuma yankin Gabas ta Tsakiya.
Cire kwaroron roba yayin Jima’i
Lokacin da shirin Michaela Coel na ‘I May Destroy You’ ya fito a akwatunan talabijin a 2020, shirin ya samu karbuwa a wajen masu suka.
Sai dai shirin mai dogon zango da ya samu lambar yabo a Birtaniya, wanda ya tattauna da wata mata yadda rayuwa ya kasance mata bayan cin zarafinta, masu suka daga ko’ina a fadin duniya sun yi ta tattaunawa kan batun.
Maite Orsini, wata ‘yar majalisar dokokin ƙasar Chile mai shekara 34, ta ce ta kadu matuka a wani wuri na fim din, inda jaruma mai suna Arabella ta gano cewa mutumin da suke tare ya cire kwaroron roba ba tare da saninta ba lokacin jima’i.
Daga baya ta gano cewa cire kwaroron roba ba tare da sanin mutum ba, ana kwatanta shi da laifin aikata fyade a Birtaniya da Jamus da Canada da kuma jihar California da ke Amurka.
“Bani da masaniyar cewa hakan cin zarafi ne, sai bayan da na kalli hakan a cikin fim din,’’ a cewar miss Orsini, wata lauya da kuma ta yi karatun digiri na biyu a fannin kare jama’a.
Tun da ba a dauki batun cire kwaroron roba yayin jima’i a matsayin laifi ba a Chile, babu hakikanin alkaluman yawan aikata hakan daga wajen hukumomi.
Sai dai, a yayin da miss Orsini ta yi magana da abokan aiki da ‘yan uwa, an gano cewa lamarin ya tsallake iyakoki – inda babu wata doka da za ta bi hakkin wadanda aka ci wa zarafi.
Ta ce ya kamata a samar da doka a Chile da za ta hukunta duk wanda ya cire kwaroron roba yayin jima’i.
“Mun sha yin muhawara kan yadda za mu kira sunan lamarin da harshen Sifaniya, sai dai na ki amince da hakan.
Ina so wadanda aka ci zarafinsu su gane cewa ana amfani da kalmar a harshen ingilishi, kuma za su iya zuwa shafin intanet domin samun bayanan da suke so.’’
Asalin hoton, Maite Orsini
Dokar da miss Orsini ta gabatar ya samu karbuwa a majalisar dokokin ƙasar ta Chile a watan Janairu, inda yanzu kuma ya wuce zuwa majalisar dattawa. Dokar dai za ta sanya batun cire kwaroron roba lokacin jima’i zama babban laifi – da za a hukunta duk wanda ya aikata hakan.
Za a iya ganin hakan a matsayin yunkurin mata na kara iko kan harshe, a cewar Dr Tranchese.
‘Idan ka tuna abubuwa kamar kamusu, wa yake yin kamusu? A tarihi, maza ne ke buga su.
”Ba a barin mata su yi rubuce-rubuce ko zama lauyoyi ko kuma likitoci, inda maza suka mamaye wadannan bangarori. ”
Miss Orsini ta amince cewa harshe na da rawa da zai taka wajen kare mata da suka fuskanci cin zarafi.
“Ina ganin bayyana dabi’u da ba kowaye ya san su ba, zai iya sanya wadanda suka fuskanci cin zarafi sanin cewa an ci musu zarafi,’’ in ji miss Orsini.
“Ina son ganin an samar da wata babbar doka kan batun cire kwaroron roba yayin jima’i, domin wayar da kai cewa akwai wannan nau’i na cin zarafi, saboda mata da ƙananan yara su gane lokacin da aka aikata musu hakan. Doka ta haramta hakan, a don haka za su iya kai rahoto a kan batun.”
Daukar hotunan mata ta kasan siketinsu ba tare da saninsu ba
Ana amfani da harshe don nuna yadda mata ke ji yayin da suke ƙara shiga hadari a wuraren jama’a, a cewar wani dan siyasar Arewacin Ireland.
An sanya hannu kan sabuwar dokar hukunta masu aikata cin zarafi kan mata a Arewacin Ireland a watan Maris, wacce tsohuwar ministar shari’a a ƙasar, Naomi Long ta gabatar.
Dokar na kunshe da sabbin kalmomi kamar ‘downblousing’ – da ya kwatanta batun daukar hotunan mata ta kasan mata ba tare da saninsu ba.
“Wannan wani nau’i ne na cin zarafi,’’ in ji miss Long. ‘Yunkuri ne na kaskantar da mata da kuma sanya musu tsoro.’’
A baya, ba a bayyana hukuncin laifin ba a cikin doka, wanda hakan ya zama abu mai wahala ga wadanda aka ci wa zarafi da kuma ‘yan sanda na yadda za a hukunta masu laifin.
“Abin takaici ne idan ka tuna cewa an taba cin zarafinka, inda ko da ka je wurin ‘yan sanda basu tabbacin cewa ko aikata hakan laifi ne ba.’’
Asalin hoton, Neil Harrison
An yi ta tattaunawa kan harshe da kuma kalmomin cin zarafi daban-daban, in ji miss Long.
”An kuma tattauna kan cewa ko kayan da matan ke sanyawa don gano irin zarafinsu da aka yi musamman ko taba musu mama da sauransu.
“Ina ganin akwai bukatar gano cewa mutane basa zuwa don daukar hotunan maza a kasan rigunansu. Hakan bay a faruwa, ba abu bane.’’
Arewacin Ireland ta kasance ta farko wajen bijiro da dokar da ta amince cewa daukar mata hoto a kasan siketinsu babban laifi ne a Birtaniya.
Arewacin Ireland ta bukaci Ingila da Wales su ma su yi irin hakan.
“Babu bukatar duba harshe a nan, abin da ya kamata shi ne yanda muke kwatanta wadannan abubuwa. ‘Hakan zai bai wa al’umma damar sanya wa wani abu da suka san cewa ba shi da kyau suna.
Ta ya ya harshe ke aiki?
Aikin farfesa Lera Boroditsky shi ne bincike kan yadda mutane ke da dabara, inda bangare mafi muhimmanci na amsar ita ce harshe, in ji Lera.
“Harsuna na cikin abubuwan da za mu iya sauyawa zuwa yanda muke so. Akwai tambayoyi da yawa da ke nuna yadda harsuna da muke magana da su ke sauya irin tunani da muke, da kuma irin kokari da muke na canja yanda muke magana domin canja tunanin mutane a kusa da mu,’’ a cewar Boroditsky.
Masana kimiyya sun duba dangantakar da ke tsakanin harshe da tunani da kuma yadda hakan ke a cikin al’umma.
“Alal misali, an dauka cewa za a tambayi wadanda aka ci zarafi a kotu, kamar cewa ‘shin a lokacin ne ya sumbace ki? Sumbata abu ne mai kyau ga yawancin mutane, amma ba a lokacin da aka tirsasawa wani ba.
Saboda haka idan aka kira shi da ‘tirsasawa’, wadanda aka aikatawa hakan na ganin lamarin a cikin wani yanayi.
Tirsasa yin jima’i
Mata ka iya fuskantar ci zarafi na jima’i daga wajen mazajen su
A kullu yaumin, Lamya Lotfey na haduwa da matan da ake cin zarafinsu a Masar, wanda ya hada da tirsasawa mata yin jima’I da mazajen s uke yi.
”Matsalar ita ce matan basa iya gane cewa hakan cin zarafi ne a gare su, in ji Loftey.
Loftey, wacce ta kasance shugabar shirye-shirye a gidauniyar New Women, ta ce ta sha shiga tsakani da kuma tseratar da matan da aka ci wa zarafi.
Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya na 2018, ya nuna cewa kashi 30 na mata ko masoya ‘yan shekara 15 zuwa 49, sun fuskanci cin zarafi ko daga waje ko kuma daga mazajen su na aure a tsawon rayuwarsu.
Yawancin matan da suka fuskanci batun tirsasa musu yin jima’i, su basa ma sane da hakan. Shin wa za su ka iwa ƙara kuma a kan me? Kamar yadda Loftey ta tambaya.
Mazan da aka kama da laifin aikata fyade a Masar, za su fuskanci hukuncin daurin rai-da-rai ko ma hukuncin kisa – sai dai babu dokar hukunta wadanda suka tirsasawa matansu yin jima’i a dokokin ƙasar.
Kungiyar miss Loftey, ya taimaka wajen bijiro da bukatar sanya hukuncin masu tirsasawa matansu yin jima’i.
Karo na biyu da suke gabatar da irin wannan bukatar gaban majalisar dokokin ƙasar – inda take jira domin fara tattaunawa kan dokar a zauren majalisar.
”Aikata fyade babban laifi ne a cikin al’umma, hakan ne ya sa ake ci gaba da gwagwarmayar ganin mazaje ma sun daina tirsasawa matansu yin jima’i,” in ji miss Loftey.
Asalin hoton, Lamya Lotfey
Lamya Lotfey ta sadaukar da aikinta wajen tabbatar da cewa mata sun kaucewa fadawa cin zarafi
Kungiyoyin kare hakkin dan adam a Masar, sun fara amfani da kalmar tirsasawa matan aure jima’I ne a shekarun 1880, sai dai hakan ya fi ta’allaka kan wasu tsirarun mutane, a cewar Loftey.
Ta ce abubuwa sun fara canzawa sannu a hankali.
Wani ya fada mani cewa, ‘Shin idan muka ce hakan na faruwa da mu, zai sa su dauke mu da muhimmanci? Amma kafin nan, ba a damuwa da tirsasawar, kamar abun ba ya faruwa.”
Wata masaniya kan harshe, Dr Alessia Tranchese, ta nuna irin rawar da harshe zai taka, da zai taimaka wa al’umma.
“Ina ganin wadannan kalmomi sun bai wa mata damar ganin ba a yi watsi da labaran da suka bayar ba na cin zarafi.