Yadda Tabarbarewar Tattalin Arziki da Faduwar darajar Naira Suka Shafi Farashin Raguna a bana


 

rams-e1473412384285

 

A yayin da bikin babban sallah ya matso kusa, masu sayen raguna sun yi karanci a kasuwannin a fadin Nijeriya a sakamakon tsadar da ragunan suka yi.

Wani mai sayarda ragunan a kasuwar Dei-Dei da ke birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa a wannan shekara ana sayarda ragunan ne tsakanin naira dubu 60 da dubu 400,000, ya kara da cewa hakan ya sanya ragunan su fi karfin mutane da yawa a irin wannan yanayi da kasar ta samu kanta.

Malam Usman ya fadawa wakilin jaridar Premium Time’s cewa adadin wadanda ke sayen ragunan sun ragu sosai idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.

Masu sayarda ragunan sun bayyana cewa faduwar darajar naira, tabarbarewar tattalin arziki da damuna su suka haifar da hauhawan a farashin ragunan.

Sun kuma ce duk da dai kasuwar ba ta tafiya a halin yanzu, suna jira zuwa kwana daya ko biyu kafin sallah su ga yadda kasuwar za ta canza.

Haka kuma akwai wadanda suka ce suna shigo da ragunan su daga jamhuriyar Nijar, kuma a wannan shekarar suna canja Cefa 200 a kan naira 645 a maimakon naira 300 da suka canza a bara.

 

Suka ce akwai kuma matsalar sufuri da shima kudin ya karu. Duk wadannan abubuwa sun taimaka wajen sanya ragunan su fi karfin talaka.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like