
Asalin hoton, ARETHA PRETORIUS
Aretha da Chris da kuma ɗiyarsu Bella na shirin komawa wani karamin gida, amma kuɗin hayarsa ya kai kashi 32
Watannin Febrairu da kuma Maris sun kasance masu wahala ga Aretha Pretorius.
Ita da mijinta sun shafe tsawon makonni suna yawo a Dubai domin neman sabon gidan da za su shiga.
Sun zauna a wani gida mai ɗaki uku da ke tsakiyar birnin tun 2019.
Sai dai a shekara da ta gabata, masu gidaje suka sanarwa iyalai cewa su tashi daga wajen da suke zaune, inda ya ce ba zai ƙara ba su haya da kuɗi kalilan ba idan na su ya kare a watan Maris saboda yana shirin komawa gidan da zama.
Sun fara neman wani gida ne a kusa da wajen da suke zaune, sai dai, sun kaɗu lokacin da jin cewa kuɗin haya a shekara ya haura zuwa kashi 75 kan $34,000 da suke biya a baya.
Sun faɗaɗa neman gidan zuwa wasu wurare a birnin, sai dai sun ƙasa samun gida daidai da kuɗinsu.
Daga baya, sun samu wani karamin gida wanda yake da nisa da tsakiyar birnin Dubai, amma za su biya kuɗi $45,000 – kashi 32 sama da kuɗin hayar da suke biya a baya.
”Mun shafe tsawon makonni muna ta neman gida. Sai dai ba mu da zaɓi illa aminta da ɗan gidan da muka samu. A yanzu za mu zauna cikin karamin gida da kuma biyan kudi da yawa,” in ji Aretha.
Gidan zai kasance na biyar da Aretha da Chris suka zauna a ciki a Dubai tun bayan zuwansu daga Afirka ta Kudu a 2011. Kasuwar harkar gidaje a Dubai ta yi ta sauyawa cikin gwamman shekaru da suka gabata.
Sai dai Aretha ta ce ba su taɓa shan wahala wajen neman gida ba kamar wannan karo.
“Kuɗaɗen haya sun ƙaru a ciki n shekaru 10 da suka wuce, amma ko da haka ba a wahala wajen neman gida kamar yadda yake a yanzu,” in ji Aretha.
Asalin hoton, Getty Images
Kusan kashi 90 na al’ummar Dubai miliyan 10 sun kasance ƴan ƙasashen waje
Karamin farashin kuɗin haya a Dubai ya kai kashi 35 a shekara da ta gabata, a cewar cibiyar hada-hadar gidaje ta Betterhomes.
Ba mutanen da ke neman manyan gidajen haya ne kaɗai ke shan wahala ba. An samu ƙaruwar kuɗin haya a dukkan fannoni.
Tashin kuɗaɗen haya na ƙara janyo wahala ga ƴan ƙasashen waje da ke zama a Dubai musamman ganin cewa sune kashin bayan tattalin arzikinta.
Kusan kashi 90 na al’ummar Dubai miliyan 10 ƴan ƙasashen waje ne.
Ƙaruwar kuɗin hayar ya tilasta wa mutane irin Waquar Ansari barin Dubai zuwa birnin Sharjah mai makwaɓtaka, wajen da kuɗin ke haya ke da sauki.
Waquar da iyalansa suna zama ne a cikin gida mai ɗaki ɗaya da ke kudancin Dubai, inda suke biyan $9,500 a shekara.
Lokacin da kuɗin hayarsa ya kusa ƙarewa a watan da ya gabata, mai gidan ya so ya ƙara $3,000 a kan kuɗin hayar.
Tun da farko, Ansari ya nemi sabon gida a wani wuri na daban, amma kuɗin ya ƙaru da kashi 40.
“Ina da niyyar biyan ƙari ashi 10-15, sai dai na duba wasu wurare a Dubai, amma ban samu gida a farashin da nake so ba. Zaɓi ɗaya ya rage min, shi ne komawa Sharjah,” in ji Ansari.
Asalin hoton, BETTERHOMES
Richard Waind na cibiyar hada-hadar gidaje ta Betterhomes ya ce yawan mutanen suke komawa Dubai ya fi yawan gidajenda ake da su a yanzu
Babban Manajan cibiyar harkar gidaje ta Betterhomes, Richard Waind, wanda ke zama a Dubai, ya ce mutanen da ke zuwa Dubai sun fi yawan gidajen da ake da su.
“Akwai mutane da yawa waɗanda ke zuwa Dubai idan aka kwatanta da gidajen da ake da su a birane da suke son zama. Ana samun tsaiko wajen samun gida wada kuma ke ƙara kuɗin haya,” in ji Waind.
A tsarin dokokin yaki da ƙarin kuɗin haya a Dubai – ƙara farashi zuwa wani mataki – na bai wa masu gidaje damar ƙara kuɗaɗen haya ga mutanen da suka kama gidaje da kashi 20.
Masu gidajen ba su da damar ƙorar ƴan haya ba tare da wata ƙwakkwarar hujja ba.
Sai dai masu gidajen haya da dama waɗanda ba su so a ambaci sunayensu, sun faɗa wa BBC cewa an ba su sanarwar ficewa daga wajen masu gidaje waɗanda suka ce su ma suka ce suna son komawa gidajen da zama.
Amma waɗanda suka kama hayar, sun yi iƙirarin cewa hakan ba gaskiya bane, inda suka ce masu gidajen na son bayar da su ga wasu mutane a kan babban farashi.
Sai dai ba kuɗin haya ne kaɗai ya tashi a Dubai ba – kuɗin sayan gidaje ma ya yi matukar tashi.
Kuɗin hayar gidaje ya kasance a kashi 35 a 2022 ida aka kwatanta da 2020, lokacin ɓullar annobar korona, lokacin da kuɗin ya ƙaru da sama da kashi 50, a cewar kamfanin harkar gidaje ta Savills.
Kuɗin ƙasar Rasha ya kasance abin da ya janyo farashin haya ke ƙara tashi a Dubai, tun bayan soma yakin Ukraine a bara, a cewar Katie Burnell, darekta a kamfanin harkokin gidaje ta Savills da ke Dubai.
Dubai ta zamo wuri da hamshaƙan masu kuɗi da ƴan ƙasuwan ƙasar Rasha ke zuwa don neman mafaka. Yawancin matasa ƴan asalin Rasha su ma sun koma birnin, inda suke neman wuraren aiki.
Kamfanoni da dama sun kwashe ma’aikatansu daga Rasha zuwa Dubai.
Asalin hoton, SAVILLS
Kuɗin ƙasar Rasha ya kasance abin da ya janyo farashin haya ke ƙara tashi a Dubai, a cewar Katie Burnell na kamfanin Savills
Ƴan ƙasar Rasha sun kasance waɗanda suka fi zuba jari daga waje a harkar gidaje a Dubai a bara.
“Akwai takunkumai da dama a kan ƴa Rasha musaman kan wajen da za su zauna ko kuma sayen kadara. Ba su da wannan matsala a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. A nan suna iya yin kasuwanci yadda suke so,” in ji MS Burnell.
“Saboda wannan damar, ba su damuwa da farashin kuɗin gida, kuma suna shirye don su biya a kowane farashi.”
An kiyasta cewa dubbban mutane ne suka bar Rasha tun soma yaki da Ukraine, duk da cewa babu wani rahoto da ya bayyana ainihin alkaluman.
A cewar wani rahoto daga mujjalar Forbes ta ce ƴan asalin Rasha 700,000 ne suka bar ƙasar tun bayan da shugaba Putin ya bayar da umarnin zirga-zirga na takaitacciyar lokaci ko kuma kiran da ya yi na shiga aikin soji a watan Satumban bara.
Sai dai fadar Kremlin ta musanta akaluman da mujjalar ta fitar.
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ba ta nuna goyon baya ba ko kuma amincewa da yakin da ake yi a Ukraine. Ba ta sanya wa Rasha takunkumi ba ko kuma sukarta tun bayan mamayar Ukraine.
Ta ci gaba da bai wa ƴan Rashar da ba a saka wa takunkumi ba biza, sai dai ƙasashen yamma da dama sun kakaba wa Rashar takunkumi.
A watan da ya gabata, Babban Bankin ƙasar ya bai wa bankin MTS mallakin Rasha lasisin fara aiki. Ƴan Rasha da dama na fuskantar wahalhalu wajen buɗe asusun banki da kuma aika kuɗi a Dubai saboda takunkumin ƙasashen yamma kan bankunan Rasha da dama.
Tun ɓarkewar annobar korona, UAE ta bijiro da tsarin biza na dogon lokaci, inda hakan ya kawo karshen buƙatar wanda zai ɗauki nauyin mutum – wanda ya taimaka wajen janyo hankalin ɗimbin masu zuba jari da ma’aikata da ƴan kasuwa zuwa ƙasar.
Yadda ƙasar ta magance korona ya taka rawa matuka wajen ƙara janyo masu zuba jari daga ƙasashe da dama a faɗin duniya.
Dubai ta buɗe wuraren yawon buɗe da cire takunkumi da ta saka a 2020 annobar korona, lokacin da yawancin ƙasashe a Turai ke cikin dokar kulle saboda korona.
Asalin hoton, Getty Images
Kuɗin sayen gidaje a Dubai ya kai kusan $56.6bn a bara – wanda ya kai kashi 80 a 2021
Dubai ta ce an sayar da gidaje sama da 86,000 a bara, inda alkaluman suka ɗara wanda aka samu a 2009 da ya kai 80,000.
An sayar da gidaje da kuɗinsu ya kai kusan $56.6bn a bara, inda aka samu kashi 80 sama da na 2021.
Richard Waind ya ce abubuwan da suka faru a duniya a cikin shekaru uku da suka gabata, ciki har da annobar korona da kuma yaƙin Ukraine, sun ƙara tabbatar da matsayin Dubai na kasancewa mai arziki, da sanya kasuwar harkar gidaje ta yi sama.
“Dubai na da tsaro yadda ya kamata da saukin yin kasuwanci da kuma kwanciyar hankali. Wannan na cikin abubuwan da suka sanya mutane daga ƙasashe da dama ke hijira zuwa nan saboda damarmaki”
A shekara da ta gabata, masu harkar gidaje sun sanar da shirin gina sabbin gidaje domin ya daidaita da ƙaruwar bukatansu da mutane ke yi.
Sai dai mista Waind na sa ran cewa tsadar kuɗin haya zai ci gaba da kasancewa har na akalla watanni 18-24 kafin a fara gina sabbin gidaje da za su zo domin rage yawan bukata wajen mutane.
Akwai damuwar da ake nunawa cewa muddin kuɗin haya ya ci gaba da ƙaruwa, mutane za su ƙasa samun gida, abu kuma da zai janyo da yawa daga cikin mutane su fice daga Dubai zuwa wasu birane a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan.
“Eh, akwai yiwuwar hakan, wanda kuma ke da muhimmancin ganin cewa kuɗin haya ya fara sauka nan da lokaci ƙankani,” in ji mista Waind.