Yadda Wata Kotu Ta Yankewa Matashin Daya Saci N500 A Jikin Gawar Da Tayi Hatsari Hukuncin Watanni Uku  A Gidan YariWata kotun majestire dake garin Minna babban birnin jihar Neja a ranar Talatar da ta gabata ta yankewa wani matashi mai suna Musa Isa dan shekaru 25 wanda ke aikin gadi hukuncin watanni uku a gida kaso sakamakon satar naira dari biyar da ya yi a aljihun wata gawa da ta yi hadari.

Dan sanda mai gabatar da karar, Sufeto Gunduma Ibrahim ya bayyanawa kotu cewa, wanda ake tuhuman wanda ke zama a yankin Rukunin Gidaje na M.I Wushishi dake garin Minna, ya aikata laifin ne a ranar Asabar din da ta gabata da misalin karfe hudu na yamma.

Sufeto Ibrahim ya kara da cewa wanda ake tuhuman ya je wurin da hadarin ya auku a Minna ne a matsayin wanda zai ceci wadanda hadarin ya shafa.

Dan sandan ya ce maimako wanda ake zargin ya ceci wadanda hadarin ya shafa, sai ya soma caje jikin daya daga cikin wadanda suka rasu sakamakon hadarin, inda ya zare masa naira dari biyar.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne a take inda aka mika shi ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

Bayan karanto tuhumar da ake yi masa, wanda ake zargin ya amsa laifinsa tare da neman gafarar kotun domin ta yi masa sassauci.

Bayan sauraren karar Mai shari’a Misis Maryam Kings ta yankewa Isa hukuncin watanni uku a gidan yari ko kuma ya biya tarar naira dubu ashirin.

You may also like