
Asalin hoton, Swastika Pal
Matar ta ce za ta yi duk iyawarta don hukunta wanda ya yi wa ‘yarta fyade
A shekarar da ta gabata, aka faɗa wa wata mata a jihar Bihar da ke kudacin Indiya cewa mutumin da ya yi wa ‘yarta fyaɗe ya rasu saboda haka an rufe ƙarar da aka shigar kansa. Sai dai, ta sa shakku kan haka wanda kuma ya kai ta gano gaskiyar lamarin, inda hakan ya janyo sake dawo da ƙarar don ƙwato wa ‘yarta ta hakki.
Wakilin BBC Soutik Biswas ya binciko ainihin gaskiyar lamarin.
A wata safiya mai cike da kaɗawar iska a watan Febrairun bara, wasu mutane biyu suka iso wajen da ake ƙona gawarwaki don binnesu a gabar kogin Ganges, da ya kasance kogi mai tsarki a Indiya.
Sun je wurin ne domin halartar jana’iza ta al’ada da ‘yan addinin Hindu ke yi. Mutanen na ɗauke da itace a hannunsu, sai dai, basa rike da gawa. Isar su wurin ke da wuya, sai al’amura suka canza salo.
Mutanen sun gina wani wajen kunna wuta, sannan, ɗaya daga cikinsu ya shiga wurin, ya kuma rufe kansa da wani farin kyalle tare da rufe idonsa. Ɗayan mutumin kuma, ya yi ta saka itace har sai da ya rage kan mutumin na farko shi kaɗai ake iya gani a waje.
An ɗauki wasu hotuna guda biyu na wannan lamari. Ba a san hakikanin wanda ya ɗauki hotunan ba ko cewa watakila akwai wani mutum na uku da ke wurin.
Mutumin da aka ce ya mutu mai suna Niraj Modi, ɗan shekara 39 ne da ke koyarwa a wata makarantar gwamnati. Ɗayan mutumin kuma mahaifinsa ne Rajaram Modi da ke da shekara 60 kuma manomi.
Daga nan Rajaram Modi ya yi tafiya zuwa wata kotu da ke da nisan kilomita 100 tare da rakiyar lauya, inda ya sa hannu a kan wata takarda ta ratsuwar cewa ɗansa Niraj Modi ta rasu a ranar 27 ga watan Febrairu a garin mahaifarsa.
Ya kuma gabatar da wasu hotuna biyu daga wajen da ake ƙona gawarwakin da kuma rasitin itace da suka saya don ya zama hujja.
Asalin hoton, Swastik Pal
Wannan shi ne hoton mutumin da aka ce ya rasu mai suna Niraj Modi wanda kuma ake zargi da yi wa wata yarinya fyaɗe
Wannan ya faru kwana shida bayan ‘yan sanda sun gabatar da tuhume-tuhumen fyaɗe a kan Niraj Modi. Ana dai zargin Modi da yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyaɗe a watan Oktoban 2018, wadda kuma ta kasance ɗalibarsa.
Mutumin ya afka wa yarinyar ne a cikin gonar rake lokacin da take ciki ita kaɗai, inda ya ce ya naɗi abin da ya faru tsakaninsu kuma zai wallafa shi a kafafe sada zumunta.
An kama Modi ne jim kaɗan bayan da mahafiyar yarinyar ta shigar da ƙorafi, sai dai, an sake shi bayan shafe watanni biyu a gidan yari bayan da aka ba da belinsa.
Abubuwa sun tafi da sauri a bara bayan sanar da mutuwar Niraj Modi. Watanni biyu baya da mahaifinsa ya faɗa wa kotu kan rasuwar tasa, hukumomi suka gabatar da shaidarsa ta mutuwa. A watan Mayu, kotun ta rufe batun ƙarar saboda wanda ake zargin ba ya raye.
Mahaifiyar yarinyar ce kaɗai ta yi zargin cewa malamin Niraj Modi ya yi karyar cewa ya mutu, inda kuma ya tafi ɓuya don kaucewa hukunci.
Asalin hoton, Swastik Pal
Rajaram Modi, the father of Niraj Modi, was also seen in a picture near the pyre
“Daga lokacin da naji cewa Niraj Modi ya rasu, na sani ƙarya ne. Na san cewa yana raye,’’ in ji mahaifiyar yarinyar.
Mutum bakwai cikin goma da ke mutuwa Indiya, na faruwa ne a kusan ƙauyuka 700,000 na ƙasar, sannan ana samun ƙaruwar mutane da ke mutuwa a gida idan aka kwatanta da na birane.
Akwai wata doka da aka yi shekaru 50 da suka wuce da ta tilasta yin rajistar waɗanda aka haifu da kuma waɗanda suka mutu – sai dai, ba a yin haka a bangaren waɗanda suka mutu.
Idan mutum ya mutu a wani ƙauye a jihar Bihar, ɗan uwansa zai gabatar da lambobin da ke nuna shaidar yatsunsa da kuma sa hannun mazauna ƙauyen guda biyar waɗanda suka tabatar da cewa ya mutu.
Ana bai wa shugabannin yankin waɗannan abubuwa, inda mambobinta da ya kunshi wani mai rajista, shi zai duba takardun – idan har komai ya tabbata daidai yake – sannan zai miƙa takardar shaidar mutuwa a cikin mako ɗaya. “Mutanen ƙauyenmu duka a haɗe suke ba a warwatse ba. Kowa ya san kowa.
Da wuya ace ba a ji ba ko kuma ba a ga wanda ya mutu ba,’’ in ji Jai Karan Gupta, lauyan wadda aka yi wa fyaɗe.
Rajaram Modi ya gabatar da lambobin shaidar hannu na wasu mutane biyar daga ƙauyensu da takardar sa hannu da ke nuna cewa ɗansa ya rasu, inda kuma ya karɓi shaidar mutuwar ɗan. Takardun basu bayyana abin da janyo rasuwar tasa ba. Rasiti daga shagon sayar da itace ya nuna cewa ya mutu saboda wata cuta.
A wata rana a watan Mayun bara, mahaifiyar yarinyar ta kai ga gano ta hannun wani lauya cewa an rufe ƙarar da aka shigar kan Modi saboda ya mutu.
Asalin hoton, Swastik Pal
The girl has stopped going to school after the attack and spends most of her time at home
“Amma ta ya ya babu wanda ya san da mutuwar malamin? Me ya sa ba a yi abubuwan al’adu da ake y iba na duk wanda ya mutu? Me ya sa babu maganganu kan mutuwar? Mahaifiyar yarinyar ta tambaya.
Ta ce ta bi gida-gida don gano daga wajen mutane ko cewa Niraj Modi ya mutu. Babu wanda ya ji labarin. Daga nan ta tafi zuwa kotu don roƙon a yi bincike kan lamarin, sai dai, alkalai sun buƙaci a gabatar da hujjoji da ke nuna cewa malamin yana raye.
A tsakiyar watan Mayu, ta shigar da ƙarar wani babban jami’i a yankin, inda ta ce hukumomin ƙauyen sun bayar da shaidar nuna mutuwa ne ta wasu takardu na bogi da aka kai musu, don haka ya kamata a yi bincike kan hakan.
Daga nan abubuwa suka fara aukuwa da sauri daga lokacin.
Jami’in ya bayar da umarnin yin bincike da kuma faɗa wa jagororin ƙauyen. Mambobin sun buƙaci ƙarin hujjoji daga wajen Rajaram Modi kan mutuwar ɗansa, kama daga hotunan mamacin da wurin da aka binne gawarsa da bukukuwan al’ada da aka saba yi da kuma sabbin hujjoji daga wajen wasu mutane biyar.
Mambobin ƙauyen sun ziyarci gidajen mazauna yankin guda 250. Da alama babu wanda ya ji labarin mutuwar Niraj Modi. Aske gashin kai, wata al’ada ce ta zaman makoki a addinin Hindu da ɗan uwan wanda ya mutu ke yi. Duk da haka, babu wani daga cikin ‘yan uwan Modi da ya aske kansa.
Asalin hoton, Swastik Pal
Rajaram Modi’s death certificate was cancelled by the authorities in May last year
“Ko da ‘yan uwan Niraj Modi ma basu da labarin mutuwarsa ko wajen da yake. Sun ci gaba da faɗin cewa muddin ya mutu, to da an gudanar da bukukuwan al’ada a gida,’’ in ji Rohit Kumar Paswan, jami’in ɗan sanda da ke bincike.
Mambobin ƙauyen sun nuna shakku kan iƙirarin Rajam Modi. Ya gaza gabatar da sabbin hujjoji kan mutuwar ɗansa. “Lokacin da muka yi masa ƙarin tambayoyi, bai bayar da gamsasshiyar amsa ba,’’ in ji Dharmendra Kumar, sakataren hukumar yankin.
Bincike ya gano cewa Niraj Modi ya yi karyar cewa ya mutu sannan shi da mahaifinsa sun gabatar da takardun bogi domin samun shaidar mutuwa.
‘Yan sanda sun gano cewa malamin makarantar ya ɗauki shaidar lambobin yatsu na iyayen ɗalibansa guda biyar, inda ya sa hannu ta bogi a wata takarda inda yake buƙatar shaidarsa ta mutuwa. Ya faɗa wa iyayen cewa yana son shaidar yatsunsu ne don bai wa yaransu tallafin karatu.
A ranar 23 ga watan Mayu, hukumomi suka soke shaidar mutuwar Niraj Modi. ‘Yan sanda sun kama mahaifinshi da kuma zarginsa da gabatar da takardun bogi. “Ban taɓa yin bincike kan irin wannan lamari ba tsawon rayuwata,’’ in ji Mista Paswan. “Abin da suka shirya ya so karɓuwa, amma bai samu shiga ba.”
A watan Yuli, kotun ta sake buɗe ƙarar, inda ta ce “an yaudareta da bayar da bayanan ƙarya” saboda wanda ake zargin ya kaucewa hukunci. Mahaifiyar yarinyar, a fafutuka da take na gano malamin, ta tafi zuwa kotu domi ganin an kama shi.
Asalin hoton, The News Post
An yanke wa Niraj Modi (a tsakiya) ɗaurin shekara 14 a gidan yari kan laifin yi wa yarinyar fyaɗe
A watan Oktoba, Niraj Modi, ya kaik ansa ga kotu, watanni tara bayan sanar da cewa ya rasu. Yayin jin ƙarar a gaban kotu, ya kare kansa ta hanyar musanta zargin aikata fyaɗe da ake masa. A yanzu ya fice daga kotun cike da ɓacin-rai da igiya a gefensa.
A watan da ya gabata, kotun ta samu Niraj Modi da laifin aikata fyaɗe, inda ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 14 a gidan yari. Ta kuma bayar da umarnin biyan wanda aka yi wa fyaɗen diyyar rupee 300,000. Mahaifinsa kuma na gidan yari ne inda yake fuskantar zarge-zarge da suka haɗa da zamba da kuma rashin gaskiya, wanda ke ɗauke da hukuncin ɗaurin shekara bakwai a gidan yari. A yanzu, ana zargin Niraj Modi da mahaifinsa kan batun gabatar da takardun shaidar mutuwa na bogi.
“A cikin sama da shekara uku, na tafi zuwa kotu don tabbatar da cewa an hukunta wada ya yi wa ‘yata fyaɗe. Sannan akwai ranar da lauyansa ya faɗa min cewa ya mutu. Ta ya ya za a ce mutum ya mutu haka nan kawai?” in ji mahaifiyar yarinyar.
“Lauyan ya fada min cewa za a kashe kuɗi da yawa wajen sake yin ƙara don bayar da hujjar cewa kariya ne bai mutu. Wasu sun faɗa min cewa wanda ake zargin zai fita daga gidan yari, ya kuma ɗauki fansa.
“Ban damu ba. Na ce za kawo kuɗin. Bana fargaba. Na faɗa wa alkalin da kuma jami’ai.”
Asalin hoton, Swastik Pal
Mahaifan yarinyar na rayuwa ne a wannan ƙauye da ke jihar Bihar
A 2019, Firaminista Narendra Modi, ya sanar da cewa kashi 100 na ƙauyukan Indiya sun bayyana cewa basu da sauran mutane da ke bahaya a waje bayan wani gagarumin shirin gwamnati na gina wuraren bahaya. Duk da haka, gidaje da dama – haɗe da uwaye – basu da wuraren yin bahaya.
Wannan dalili ne ya sa ‘yarta ta tafi yin bayaha a wata gonar rake da ke kusa.
A lokacin ne kuma Niraj Modi yaje zuwa bayanta tare da toshe mata baki da kuma yi mata fyaɗe, a cewar binciken wani Alkali Kush Kumar. Niraj Modi ya kuma faɗa mata cewa kada ta yi magana kan abin da ya faru saboda ya naɗi abin a cikin hoton bidiyo, inda ya yi mata barazanar cewa zai wallafa shi, in ji Lauyan.
Asalin hoton, Swastik Pal
“My daughter’s life has shut down after the incident,” her mother says
Kwanaki goma bayan harin, a tsorace yarinyar ta gaya wa mahaifiyarta labarin.
Mahaifiyar ta je wurin ‘yan sanda. A cikin ‘yan kwanaki, ‘yarta ta ba da shaida.
“Niraj Modi ya kan yi min duka a makaranta,” kamar yadda ta shaida wa ‘yan sanda.
Yarinyar ta koma makaranta bayan kama Niraj Modi da aka yi, amma ta daina zuwa a lokacin da ya fito bayan ba da belinsa. A yanzu, ta shafe shekara huɗu bata je makaranta ba. An sayar da litattafan makarantarta ga wani mai sayar da kayan tarkace.
Yarinyar yanzu tana shafe yawan lokacinta a cikin wani ɗakin duhu.
Mahaifiyarta ta ce “Rayuwarta a matsayin ɗaliba ya kare, ina matukar tsoron in bar ta ta fita, ina fatan za mu iya yi mata aure.”