Rundunar ‘yan sandan Birnin Abuja ta kaddamar da bincike akan wani
hadari da ya faru tsakanin wata karamar mota da jirgin kasa a birnin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan birnin Abuja DSP Josephine Adeh, cikin wata
sanarwa da ta aikewa Sashen Hausa na VOA, ta ce hatsarin ya faru ne a
Chikakore da ke cikin unguwar Kubwa a birnin na Abuja.
DSP Adeh ta yi bayanin cewa jim kadan da faruwar lamarin, jami’an
‘yan sanda masu bincike daga ofishin ‘yan sanda sun ruga wurin
inda likita ya tabbatar da mutuwar mutum daya,
A halin da ake ciki rundunar ‘yan sandan birnin ta kaddamar da bincike akan
aukuwar hadarin da nufin kare aukuwar irin haka a gaba.
Dama dai akwai gine-ginen gidajen jama’a da ke daf da hanyar filin
jjirgin kasan da sau tari sai sun bi ta kan layin dogon kafin su isa
zuwa gidajensu