
Asalin hoton, Getty Images
Ciyarwa a lokacin watan azumin Ramadan na ɗaya daga cikin manyan abubuwa masu falala a cikin watan.
A cikin jerin bayanan da muke kawo muku kan azumin Ramadan, Sheikh Ahmad Ja’afar Abdulmalik na masallacin ‘yan majalisu da ke Kaduna ya yi bayani kan muhimmancin ciyarwa a watan Ramadan.
Malamin ya shaida wa BBC cewa ciyarwa na da matuƙar muhimmanci ga al’ummar musulmi musamman a lokacin watan Ramadan.
Saboda a cewarsa ciyarwar kan taimaka wajen yaye wa al’umar musulmi baƙin ciki, da abubuwan da ke damunsu ta yadda za su sauke nauyin iyalansu.
Sheikh Ahmad ya ce Manzon Allah S.A.W ya ce ”In je in bi wani mabuƙaci gidansa, in taimaka masa wajen yaye masa damuwarsa, ya fi in zauna cikin masallacin nan in yi ittikafi na tsawon wata guda”.
Falalar ciyarwa a watan Ramadan
Malamin ya ce saboda muhimmanci ciyarwa ayoyi da dama a Al’qur’ani suka sauka domin kwaɗaitar da al’umma ciyarwa a cikin watan Ramadan.
”A cikin ayoyin Allah maɗaukakin Sarki ya faɗi irin tarin ladan da ya tanadar ga masu ciyarwa a cikin musulunci”, in ji shi.
Malamin ya ci gaba da cewa ”Amma idan aka ce watan azumi ya shigo, to gaba-ɗayansa wata ne na ciyarwa”.
Haka kuma a wani hadisin Manzo S.A.W ya ce ”Wanda ya ciyar da mai azumi yana da ladan azumin, ba tare da an tauye wa mai azumin wani abu daga cikin ladan azuminsa ba”.
Sheikh Ahmad ya ce la’akari da wannan hadisi idan mutum ya ciyar da mai azumi na tsawon wata guda, kenan yana da ladan azumin wata guda, baya ga nasa shi wanda ya yi.
”Kuma lokacin da Manzo S.A.W ya fi kowanne lokaci kyauta shi ne a lokacin watan Ramadan, a lokacin da Mala’ika Jibrilu ke saukowa su yi darasin Alqur’ani a kowanne dare ” in ji Sheikh Ahmad.
Malamin ya ce bayan darasin Qur’ani da Manzon Allah S.A.W tare da Mala’ika Jibrilu ke yi cikin dare, to gaba ɗayan ranakun watan Ramadan yana yawaita kyauta.
”Sannan Manzon Allah ya fi yi kyauta a goman ƙarshe na watan Azumi,” in ji shi.
Nau’in abincin da ya kamata a ciyar da mai azumi
Sheikh Ahmad ya ce a musulunce ba a ƙayyade wani nau’in abinci da aka ce shi ne ya kamata a ciyar da mai azumi ba.
Amma a cewar malamin shi mai azumi ana son idan zai yi buɗe-baki, to ya fara da dabino, dan haka a cewarsa kamata ya yi a fara bai wa mai azumi dabino, da ruwa.
”Sannan ka bi baya da dafaffen abinci wanda zai ci ya ji nauyin cikinsa” in ji Sheikh Ahmad.
Malamin ya ƙara da cewa ”idan ka samu dama ka sayi ɗanyen abinci ka ba shi domin ya dafa a gidansa tare da iyalansa haka ake so”.
Mai azumi kawai ya kamata a ciyar?
Sheikh Ahmad ya ce a musulunci gaba-ɗaya ciyarwa na da lada, kuma taimako abu ne mai kyau a musulunci, dan haka a cewarsa ciyar da mai azumi da marar azumi duk suna da lada.
Sai dai ya ce ladan ciyar da mai azumi ya fi, kasancewar hadisi ya ce idan ka ciyar da mai azumi kana da kwatankwacin ladan mai azumin.
Kuma a cewar Sheikh Ahmad, watan ramadan wata da Manzon Allah S.A.W ya ce Allah na ninninka lada ga waɗanda suka aikata ayyukan alkairi a cikinsa.