Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Ayarin Motocin Tsohon Gwamnan Imo Ohakim
Tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedi Ohakim, ya tsallake rijiya da baya, bayan da wasu ‘yan bindiga suka budewa ayarin motocinsa wuta.

‘Yan sanda hudu daga cikin masu tsaron lafiyarsa sun rasa rayukansu a harin.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin.

Ohakim ya mulki jihar ta Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya tsakanin shekarun 2007 zuwa 2011.

Rahotanni sun ce Ohakim wanda ke tare da ‘yar sa da dansa a lokacin harin, na hanyarsa ta komawa birnin Owerri bayan ya baro garinsu.

“Ta baya suka kawo mana harin, suka bude mana wuta babu kakkautawa, na dauka zan mutu ne, ga shi ina tare da dana da ‘yata.

“Allah ne ya taimaka ni, saboda muna cikin mota mai sulke da ba ta jin harbin bindiga.” Ohakim ya ce a hirar da ya yi da jaridar yanar gizo ta The Niche.

Ya kara da cewa, maharan sun ci gaba da bin motarsu inda suka yi ta harbin tayarsu, “amma da ikon Allah muka ci gaba da tafiya a haka har muka tsere musu.”

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar Imo ba ta ce komai ba.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like