Daya daga cikin yan matan makarantar sakandaren Dapchi da Boko Haram suka saka mai suna Fatsuma Abdullahi ta bayyana yadda yan mata biyar suka mutu lokacin da ake tsare da su.
Abdullahi wacce ta yi magana da jaridar Daily Trust cikin harshen Hausa ta ce yan mata biyar sun mutu ne sakamakon turmutsutsu da aka samu lokacin da suke tafiya. ” A cikin biyar da suka mutu biyu daga ciki kawai na sani Aisha da Maimuna.”
Ta kara da cewa ya yin da suke hannun waɗanda suke tsare da su ba a ci zarafin su ba.”Sun bamu abinci a takaice mun girka abincin da kan mu lokacin da aka ajiye mu a wani wuri rufaffe inda ko da jirgin sama ba zai gan mu ba.”
A safiyar ranar Laraba ne yan ta’addar kungiyar Boko Haran su ka dawo da yan matan da suka sace daga makarantar sakandare ta yan mata dake Dapchi.