
Asalin hoton, Other
Al’ummar Najeriya sun shiga rudani na ko su ci gaba da amfani da tsofaffin kudin kasar ko kuma a’a.
Rudanin dai ya samo asali ne daga Babban Bankin kasar CBN da kuma gwamnatin tarayya bayan da suka yi gum a kan ko za su bi umarnin kotun kolin kasar na a kara wa’adin amfani da tsofaffin takardun kudi ko kuma a’a.
Da dama daga cikin al‘ummar kasar sun bayyana damuwarsu ta rashin sanin matsayar da aka cimma.
Wasu mutane da BBC ta zanta da su sun ce tun da ranar da wa’adin da CBN din ya kara na amfani da tsoffin kudin ta cika wato 10 ga watan Fabrairun 2023, gidajen mai da wasu shagunan ‘yan kasuwa suka daina karbar tsoffin takardun kudi, sai su ce wai ai an ce a daina amfani da su.
Haka suma wasu ‘yan kasuwa a Asaba ta jihar Delta, sun shaida wa BBC irin matsalar da suke ciki ta rashin sabbin kudi a hannunsu ga shi an ce wai a daina amfani da tsoffi, wannan ya sa harkoki kasuwancinsu ke fuskantar matsaloli.
Masu sayar da kayan miya a kasuwar Asaba, sun ce a yanzu kayansu sai lalacewa suke saboda babu kudi.
Rashin sanin matsayar gwamnatin tarayya da CBN, a kan ko a ci gaba da amfani da tsoffin kudi ko kuma a dakata ne ya janyo wannan rudani a tsakanin al’ummar Najeriyar.
To sai dai kuma a nata bangaren, gwamnatin Najeriyar, ta ce za ta gabatar da nata hujjoji kan dalilanta na saka wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudin kasar gaban kotun koli idan an koma zaman shari’a.
To amma duk da haka, gwamnatin ta ce za ta yi biyayya ga umarnin kotun da ya jingine wa’adin daina amfani da tsoffin kudin daga ranar 10 ga watan Fabrairun 2023 da babban bankin kasar na CBN ya saka.
Ministan shari’a na Najeriya, Barista Abubakar Malami, ya shaida wa BBC cewa, sakamakon karar da wasu gwamnonin jihohi suka shigar yanzu wannan magana ta amfani da tsoffin kudi na kotu a yanzu.
Ya ce , “Ita gwamnati a yanzu tana da hakkin yi wa kotu jawabi domin ta yi nazari a kai, sannan kuma duk wani abu da muka sani don taimaka wa kotu yanke hukunci, mun dauki matakai na gabatarwa a gaban kotun don ta yi la’akari da shi.”
Ministan na shari’a ya ce, tun da kuma kotu a yanzu ta bayar da umarnin a ci gaba da amfani da tsoffin kudi, gwamnatin hakkinta ne ta yi biyayya ga umarnin.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da majalisar magabatan kasar ta bukaci CBN da ko ya samar da wadatattun takardun kudi, ko kuma ya fito da tsoffin da ya karba domin ‘yan kasar su ci gaba da amfani da su don magance matsalolin da aka shiga a fadin kasar na karancin takardun kudi a hannun jama’a da ma bankuna.