Yadda Yan sanda Suka Fatafata Da  Yan Boko Haram a Gaya, Kano


Jami’an ‘yan sanda a Kano sun yi aman wuta ga wasu yan Boko Haram inda suka kashe mutane 3 cikinsu kuma suka kama wasu biyu.

Duk da cewa suma Boko Haram din sun maida martani a bata kashin ‘yan sanda sun sami galaba a kan su.

Wannan artabu ya faru ne da safen Lahadi a garin Gaya, dake karamar hukumar Ungoggo.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano Rabiu Yusuf ya sanar wa manema labarai cewa wani tubabben dan Boko Haram ne ya sanar musu maboyar nasu a Gaya.

Ya ce dama tun kafin ranar suna ta tara bayanai akan haka.

” Duk da cewa ba sun bude wuta akan jami’an yan sanda, basu sami nasara ba domin sai da aka kashe 3 daga cikinsu sannan aka kama wasu 2.”

Rabiu ya kara da cewa sun kama matan wasu su masu suna Ladidi da Gezawa.

Wadanda aka kama sun hada da Abba Muhammad dan kasar Nijar mai shekaru 20; Usman Buhari daga jihar Barno, 22; da Illiyasu Abdullahi daga jihar Kano, 46.

Yan sandan sun kwato bindiga karar Ak 47, Waya kiran IPAD, IPhone, kayayyakin Sojojin Sama da hotunan su sanya da kayan.

You may also like