
Asalin hoton, Getty Images
Idan bankwana da gwarzon ɗan wasan Brazil Pele ya zama fitila a ranar Litinin, jana’izar da aka yi masa a ranar Talata ya zama wani babban al’amari.
Ɗan wasan mai shekaru 82, mutane da yawa, na kiransa da ɗan ƙwalon da ya fi kowa iya ƙwallon ƙafa, kuma ya mutu a ranar 29 Disamba.
Akwatin gawar Pelen ya isa Santos a ranar Litinin, inda dubban mutane ne suka tarbi gawar sa don girmamawa a gare shi, a filin wasan tsohon ƙungiyar kwallon ƙafar sa, mutane da dama sun tsaya har dare don yin bankwana da gawar mamacin.
A ranar Talata magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa Torcida Jovem suka taru a wajen filin ƙwallon ƙafa na Urbano Caldeira gabanin a kawo akwatin gawar.
Magoya baya na ta kaɗa tuta, fara da baƙa, launin kalar ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Santos, inda dama daga cikin su ke sanye da riga mai lamba 10, da aka fi sanin Pele da ita.
Pele ne kaɗai ya ci kwallo 1,000. “Suna ta nanatawa a lokacin da jama’a ke ci gaba da buga ganga da rawa a kan tituna.
An raka gawar tasa na tsawon kilomita bakwai, a cikin titunan Santos, yayin da jirgi mai saukar ungulu ke musu rakiya ta sama.
An dauko akwatin gawarsa kan bayan mota irin ta kashe gobara, wanda al’ada ce a kasar da akan yiwa shugabanni.
An wuce da gawar ta gefen teku, da gaban gidan mahaifiyar Pele, da ta cika shekaru 100 a shekarar data gabata.
A nan ne ɗaya daga cikin dangin Pele suka buƙaci da a yi shiru, inda nan take wurin ya yi shiru, ya yin da Doña Celeste ta dunƙule hannun ta waje daya tana addu’a.
Yan kwanakin nan ya dakatar da dukkan hada-hada a birnin Santos.
“Mutum ne mai muhimmanci ga daukacin duniya, har ga matasa,” a cewar Marcia Simoes, da ke tsaye tare da ‘ya’yanta Eduardo da Mario a wajen jagorantar binne Pele. “Ina alfahari fiye da kowane lokaci, daga Santos.
“Wani yanayi da dukkan wadanda suka zo jana’izar ke ji a ransu, na cewar shi ya fi da cewa da Brazil.
“Kowa a Brazil na son ya zama irinsa, ya kwaikwayeshi,”a cewar Thiago Silva, daya daga cikin mutanen na ƙarshe a layin kafin an kammala bikin.
“Kwarai kuwa babu wanda ya iya.
” Mahaifina masoyin Pele ne, ” cewar Sandra Garcia, da ke tare da Enzo mai shekaru 11.”
“Ko wanda yake da shekaru kamar Enzo da ke da ƙarancin shekaru, Pele ya yi tasiri a zukatan matasa.” Babu wata tambaya, ya fi Cristiano Ronaldo, babu mahaɗa ko kaɗan.
“Shi ne dan wasa da ya fi kowane dan wasa iya kwallo, tsawon shekaru.”
Baya ga ƙwallon ƙafa, Pele ya hada kan ‘yan Brazil, a matsayinsa na jakadansu. A kasar da ta rabu a siyasance da tattalin arziki, mutane ba su taɓa jin wani abu saɓanin abin kirki ba.
Amma ba za a iya faɗin hakan ba ga sabon shugaban ƙasar Luiz Inácio Lula da Silva ba, da bai fi sati uku da fara zangon sa na uku ba.
Ya zo don yin bankwana da gawar Pele, jim kaɗan kafin a kammala bikin jana’izar, inda aka yi ta ihun gare shi, da kiraye-kirayen da cewa ya kamata a ce yana gidan yari.
An saki shugaba Lula daga gidan gyaran hali a shekarar 2019, bayan shafe watanni 18 a daure saboda zargin cin hanci da rashawa. An janye hukucin nasa a 2021.
Haɗuwar ‘yan ƙasar waje ɗaya don jimamin mutuwar dan wasan, abin farin ciki ne ga mutane da yawa, bayan daukar wasu kwanaki ana fama da rikice-rikice tun bayan kammala zaben shugaban ƙasar.
” Pele ya haɗe kan dukkan mu,” in ji Deofilo de Freitas, da ke tsaye a kan layin.
Shi ne na farko a kan layin a ranar Litinin, amma ya so ya sake samun damar ganin gwarzo da za’a a kai shi makwancinsa.
Pele: Brazilians react to football legend’s death