
Asalin hoton, FARAH FERRERO
Watan Ramadan lokaci ne da Musulmi ke zage damtse wajen gudanar da ibadu, ba dare ba rana don samun kusancin ubangiji.
Ibada ce da ke nuna tsantsar biyayya ga umarnin ubangiji da sadaukarwa.
Azumi na sa mawadata su ji irin zafin uƙubar yunwa da miliyoyin talakawan da ke zaune cikin ƙangin yunwa.
To sai dai rashin samun wadataccen ruwa, da isasshen bacci, da ƙarancin abinci za su iya shafar lafiyar fatar masu azumin.
Kan haka ne wani ƙwararren likitan fata mai suna Derm Doctor, da aka fi sani da Dr Muneeb Shah a shafin TikTok, ke ƙarfafa wa mutane gwiwwa kan yadda za su kula da fatarsu a lokacin watan Azumin.
Ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yaɗawa kan lafiyar fata, tare da bayyana wasu hanyoyin da yake ganin za su taimaka wajen ingata lafiyar fata a wannan wata na Ramadan.
“Mafi yawan matakan da ake bi wajen kare cutukan da ke da alaƙa da fata, na haifar da zafin fata, kuma wani bincike ya nuna cewa bin irin waɗannan matakai na raguwa a lokacin watan ramadan”, in ji shi.
A maimakon haka Dakta Shah ya bayyana wasu matakai da yake ganin za su taimaka wajen inganta lafiyar fata a watan ramadan.
Yin abubuwan da ke ƙara wa jiki danshi
Asalin hoton, Getty Images
A lokacin azumi, fatar mutum kan fuskanci ƙarancin danshi da rashin ruwa a jikinta, dan haka Dakta Shah ke shawartar mutane da su yawaita yin abubuwan da da za su ƙara wa jikinsu danshi.
“Yin alwala sau biyar a rana domin yin sallar farilla zai taimaka matuƙa wajen sanya fata ci gaba da kasancewa da danshi a jikinta”, in ji shi.
“Ku tabbatar da cewa suna jiƙa fatar jikinku bayan wanke fuskarku, saboda hakan na da matuƙar muhimmanci dan kauce wa bushewar fata”.
Kula da abinci
Asalin hoton, Getty Images
Dakta Shah ya ce wasu mutanen kan yi ƙorafin cewa fatarsu na samun matsala a lokacin azumi, kuma hakan na faruwa ne sakamakon sauyin da suke samu na abinci.
”Hakan na faruwa ne sanadiyyar abincin da suke ci ko suke sha a lokacin buɗe-baki”, in ji shi.
Ya ce a cikin azumi lokacin cin abinci ƙayyadajje ne, kuma hakan zai yi tasiri wajen samun wadataccen abincin da fata ke buƙata a jikin ɗan-adam.
Dan haka yake shawartar masu azumi da su yawaita cin abincin da zai taimaka wajen kula ta fata.
“Cin abincin da aka soya ba shi da alaƙa da ciwon fata, to amma cin kowanne abu da yawa zai iya shafar lafiyar fata”, in ji shi.
Sauƙaƙa wa kai
A lokacin azumi, yanayin cin abinci da bacci kan sauya, kuma wasu mutanen kan yi ƙoƙarin ganin sun samu lakacin biyan bashin baccinsu, ko sauya lokatan kula da lafiyar faratsu.
Mista Shah ya shawarci masu azumi da su sauƙaƙa wa kansu ta hanyar amfani da mayukan da ba su da matsala waɗanda kuma za su taimaka wajen sanya fata ta yi danshi.
Ya ƙara da cewa yawan jika fata, tare da amfani da mayukan da za su sanya fata ta yi danshi a lokacin da ake azumi, za su taimaka sosai wajen inganta lafiyar fata.
Kamar Dakta Shah, ita ma Farah Ferrero wata mai amfani da shafukan sada zumunta wajen ilimantar da mabiyanta kan yadda za su kula da lafiyar fatar su a lokcin azumin, ta ce akwai ƙarairayi masu yawa da ake yaɗawa kan lafiyar fata a yanar gizo.
Matashiyar mai shekara 29 ta shawarci mutane da su riƙa yawaita jika fatarsu da ruwa a lokacin azumin.