Kwanakin kada da fara amfani da sabon kudin na N1000 da N500 da kuma N200, bayanai sun ce an fara samun jabun Naira dubu daya da ke yawo a tsakanin ‘yan kasar.

Asalin hoton, BAYO OMOBORIOWO
‘Yan Najeriya sun fara yin tambayoyi kan ko an fara yin jabun wasu daga cikin sabbin kudin kasar.
Wannan dai na zuwa ne bayan bullar wani faifan bidiyo a kafafen sada zumunta, inda wani mutum yake kokawa kan yadda wani ya bai wa matarsa da ke sana’ar POS jabun sabuwar naira dubu daya da babban bankin kasar ya kaddamar ranar 15 ga Disambar da muke ciki.
A bidiyon mijin matar ya nuna jabun naira dubu dayan da ta gasken, ta yadda al’umma za su bambance su
Asalin hoton, BAYO OMOBORIOWO
Yadda za ku gane jabun sabon kudin
Sabon kudin dai na dauke da wasu lambobi na tsaro da za su saukaka maka gane jabun da mai kyau.
Babban bankin Najeriya ya yi bayani a shafinsa na intanet game da yadda mutane za su gani sabon kudin na gaske da jabu, da ka gan su ko ka rike su a hannu.
“Abubuwan da suka bambanta su su ne launinta da kuma yadda take idan ka rike ta a hannu, da irin tsaron da aka sanya mata da tambarin da ke jikinsu.”
CBN ya ce kalar da aka kara wa kudin wani nauyi ne na tsaro da saukin gane na gaske da jabu.
Kazalika zaren tsaro da ke jikin kudin, za ka ga kamar an rarrabe suke, amma ba a raba su ba, idan ka ga kudin a haske za ka ga akwai rubutun CBN da aka yi shi kanana a gaba da bayan kudin.
Haka kuma babban bankin Najeriya ya ce rubutu da ke jikin kudin da lambobin da ke jiki an kara musu kauri.
Sannan babban bankin ya ce sabon kudin na da wani tsaro ta yadda ba za a iya kwafin sa ba.
Dukkan wadannan alamu da babban bankin ya ambata, babu su a jabun sabuwar dubu daya, 500, da 200.
A cewar babban bankin Najeriyar masu samar da jabun kudin ba su da masaniyar wadannan matakan tsaron da sabon kudin ke dauke da su.
Yadda Babban Bankin ke sakin kudin
Asalin hoton, CBN
Babban bankin na Najeirya na dauko kudin da aka kammala buga su daga hukumar da ke kula da buga kudin kasar ta NSPM, don rarraba su ga ofisoshinsa da ke jihohi.
Su kuma su bai wa sauran bankunan ‘yan kasuwa, su kuma su bai wa al’umma, da suka je cirar kudi daga asusunsu da ke bankunan.
Asalin hoton, Others
A ranar 26 ga Octoban 2022, shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari ya amince da sake fasalin kudin da buga su, da sakin sababbin naira N200, N500, da N1,000.
Wannan sanarwa ta haifar da muhawara a tsakanin ‘yan Najeirya, kan ko babban bankin Najeriya zai bi hanyoyi da suka kamata wajen sake fasalin kudin kasar.
Hakan ya sa babban bankin na CBN fitar da wata sanarwa a ranar 29 ga Octoban 2022, cewar sun bi dokokin da suka kamata, wajen sauya tsarin kudin da shi kan aikin ya kama a ce an yi shi tun shekaru 12 da suka gabata.
Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya ce dalilin da ya sa suka sake fasalin kudin shi ne, saboda bukatar da gwamnatin tarayyar ke da shi na yaki da cin hanci da rashawa da jabun naira.
Inda ya yi fatan wannan mataki na sake fasalin nairar zai taimaka wajen rage hauhawsar farashi, da taimakawa wajen waitar da manufofin kudi, da baiwa al’umma damar samun kudi cikin sauki, don kia kasar ga tsarin takaita amfani da madarar kudi don bunkasa tattalin arzikin kasar.
A raanr 23 ga Nuwambar 2022 Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kudin ₦200, ₦500 da ₦1000 , bayan muhawarar kwan-gaba-kwan-baya da aka yi ta yi kan batun.
Haka kuma a ranar 15 ga watan Disambar nan, babban bankin Najeriyar ya gabatar da kudin da aka sabunta, don shiga hannun al’ummar kasar.
CBN ya sa ranar 31 ga Janairu, 2023 a matsayin ranar da tsofaffin kudi na N200, N500 da N1,000 za su daina aiki.
Sai dai sauran irin su ₦5, ₦10, ₦20 and ₦50 za a a ci gaba da amfani da su har bayan 31 ga watan Janerun 2023.
Hakan ya faru ne saboda yadda gwamnati ba ta canja kudin ba, da yake na leda ba. Kudaden Najeriya da suke na leda a Najeirya sun hada da ₦5, ₦10, ₦20, ₦50, wanda suke da da girman 130 X 72 mm.
Yayin da manya kudaden da irin su ₦100, ₦200, ₦500 da ₦1000) da ake buga su a kan takarda, ke da girman 151 X 78 mm.