
Asalin hoton, Getty Images
Kotun Ƙolin Najeriya ta ɗage zaman sauraren shari’ar da wasu gwamnonin jihohin ƙasar suka shigar kan ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar.
Sai dai a ranar Talata babban bankin ya fitar da wasu matakai kan yadda mutane ka iya mayar da tsofaffin takardun kuɗin a dukkan ressan bankin da ke cikin ƙasar, daga 15 har zuwa 17 ga watan Fabarairu.
A halin yanzu, ‘yan Najeriya na cikin rudani kan ko za su iya ci gaba da amfani da tsofafin takardun kudin.
Wannan matsalar ta karancin sababbi da tsofaffin takardun kudi ta shafi dukkan sassa na tattalin arzikin kasar.
Matsalar ta kai ga har wasu jama’a na zuwa bankuna domin karbar tsabar kudin kasar kamar kwandaloli domin su kauce wa asarar dukiyarsu.
Rahotanni daga wurare da dama sun nuna cewa bankuna sun daina karɓar tsofaffin takardun kuɗin, suna bayar da hujjar cewa umurni ne suka samu daga Babban Bankin na Najeriya.
Bugu da ƙari wasu masu ƙananan sana’o’in da dama sun daina amsar tsofaffin kuɗaɗen.
Matakan da za a bi wajen mayar wa CBN kuɗin?
Babban Bankin Najeriya ya samar da wata hanyar da masu tsofaffin takardun kuɗi a Najeriya ka iya shigar da kudin asusun ajiyarsu na banki.
Sai dai wannan tsarin na gajeren lokaci ne, domin zai kawo karshe ne a ranar 17 ga watan Fabrairu.
Ga yadda za a iya shigar da takardun kudin hannu CBN:
- Da farko sai ku bude wani shafin intanet na bankin na CBN a cika wani fom, inda daga nan za a ba ka wata lamba ta musamman wadda za ka rubuta kuma ka tafi da kudinka zuwa reshen babban bankin da ke kusa da ku. Amma kana iya cika fom din a harabar babban bankin.
- Jami’an tsaro za su tantance asusun da za a zuba kudaden.
- Idan akwai wata matsala, bankin zai mayar wa mai takardun kudin dukkan kudaden da ya kai bankin na CBN.
- Shigar da kudin na iya daukar mako hudu kafin a kammala.
- Akwai kuma wani sharadin na hani ga wani mutum na daban ya kai kudin da ba nashi ba bankin domin a adana su. Wanda ya mallaki kudin ne kawai ke da damar shigar da su da kansa.
Abubuwan da ake bukata su ne: lambar nan da aka samo daga fom din rajista da asusun ajiya da ba shi da wata matsala da lambar BVN ta masu asusun ajiya a Najeriya da kuma katin shaida na gwamnatin tarayyar kasar.