
Asalin hoton, Stephanie Vilchez
A watan Mayu na 2020, Fatou Ndiaye ta yi suna aka santa a fadin kasar Brazil saboda wani dalili maras dadin ji:
Budurwar wadda bakar fata ce ta samu kanta cikin yanayi na cin zarafi na wariyar launin fata a daya daga cikin fitattun makarantu masu zaman kansu na birnin Rio de Janeiro.
Shekara uku bayan wannan matsala, Fatou wadda iyayenta bakaken fata ne ‘yan ci-rani daga Senegal ta yi fitar barden-guza, inda ta zama matashiya ‘yar gwagwarmaya da ta janyo tattaunawa kan bambancin launi a kasa baki daya, a kasar da yawancin mutane ke kallon kansu a matsayin wadanda ba fararen fata ba ne.
Yayin da ake shirin bikin ranar yaki da cin zarafi da wariya ta intanet ta duniya, ranar 7 ga watan Fabrairu, matashiyar ta tattauna da BBC inda ta bayyana irin yadda ta gamu da matsalar cin zarafi na wariya ta intanet da yadda hakan ya karfafa mata gwiwa ta yaki ta’adar.
A yayin da take yi wa BBC bayani bisa ga dukkan alamu Fatou Ndiaye mai shekara 18, wadda ke da tarin ayyuka a gabanta kan tsaya ta yi tunani a kan irin abubuwan da suka faru a kanta na cin zarafi na wariyar launin fata ta intanet.
Fatou na ta kokarin tsara yadda za ta je karatunta na jami’a a Amurka, yayin da take shirya laccocin da za ta gabatar a kan wariyar launin fata a makarantu da kamfanoni a fadin kasar ta Brazil a karkashin kamfanin da take wannan aiki na Afrika Academy – wanda kamfani ne na tuntuba kan matsalolin wariya.
Yayin da duk take wadannan ayyuka matashiyar tana kuma tafiyar da shafinta na Instagram da na Twitter wadanda duka suke da mabiya sama da dubu 100.
A duk wadannan abubuwan da take yi an fi tuna ‘yar gwagwarmayar ta Brazil kan irin cin zarafin da ta fusknta na wariyar launi a fitacciyar makarantar nan mai zaman kanta ta garinsu, Rio de Janeiro, Colegio Franco Brasileiro.
Wasu daga cikin ‘yan ajinsu sun rika sanya sakonnin wariyar launin fata a shafin WhatsApp na makarantar a watan Mayu na 2020.
Duk da cewa irin maganganun cin zarafin da ke cikin wadannan sakonni ba boyayyu ba ne, har yanzu akwai wata shari’a mai tsawon gaske a kan lamarin, amma kuma iyayen Fatou sun yanke shawarar sauya mata makaranta.
Wannan batu na cin zarafin nata da ke gaban shari’a ya dauki hankalin kafafen yada labarai sosai.
Saboda Fatou ba wai kawai ta kai kara wajen ‘yan sanda ba, har sai da ta rika magana a kansa a shafukan sada zumunta da muhawara a matsayin wata hanya ta janyo muhawara da tattaunawa a kan batun wariyar launi a kasar tata ta Brazil.
Da wannan ta kuma karfafa wa matasa bakaken fata guiwa ‘yan kasar ta Brazil suma su tashi tsaye wajen wannan fafutuka ta shafukan sada zumunta da muhawara.
“Ta hanyar shafukan sada zumunta da muhawara da laccocina, ina magana akai-akai da mutanen da ke son shiga muhawarar inda suke kalubalantar abubuwan da ke faruwa,” in ji ta.
Ta ce tana fada wa mutanen da ke son shiga wannan muhawara mai zafi abu biyu ne kai tsaye a ko da yaushe.
Abubuwan kuwa su ne mutum ya kasance abin da zai fada na gaskiya ne ya faru, sannan kuma duk abin da za su sanya a shafin intanet dangane da batun su yi cikin sanin ya kamata da kamala, ”saboda akwai labaran karya da yawa yau a duniya,” ta ce.
Abu na biyu kuma shi ne, kamar yadda ta yi bayani, ”mutum ya kasance a shirye yake ya fuskanci cin zarafi sosai.”
Asalin hoton, Stephanie Vilchez
Fatou na gabatar da laccoci a makarantu da kamfanoni bayan fafutuka a shafukan sada zumunta da muhawara
Fatou ta ce, “wata babbar matsala ta intanet a wajena ita ce yadda mutane ba sa iya bambancewa tsakanin kalamai marassa dadi da ainahin kalamai na cin zarafi ko wariya.
”Mutane suna yin abu sakaka kawai su fadi duk abin da suke so ba tare da sun san cewa kalamansu na wariyar launi ko wariyar jinsi ko kuma abu ne na bata suna ba.”
Taka wa kai birki
Sama da kasashe 180 ne a duniya za su yi bikin yaki da cin zarafi da wariya ta intanet ranar 7 ga watan Fabrairu.
Kuma taken wannan shekarar ta 2023 shi ne ‘’Kuna son magana a kai? Bayar da damar tattaunawa a kan rayuwa a shafukan intanet.
Duk da cewa Fatou na ganin ya kamata kamfanonin shafukan intanet su kara tashi tsaye wajen yaki da ta’adar, tana kuma ganin akwai bukatar shi kansa mutum ya rika taka wa kansa burki.
Ta ce, ‘’kana da damar ka ki yarda da ra’ayin wani amma ba ka ci zarafinsa ba. Idan har mutane ba su kai ga fahimtar haka ba to za mu iya cewa akwai jan aiki, ba za mu samu kwanciyar hankali ba a shafukan intanet.’’
Duk da wadannan kalamai da ta yi Fatou ta jaddada shawararta ga duk wasu da za su yi irin wannan fafutuka da su kasance jajirtattu, tana mai nuni da cewa suka da sabani na daga cikin ita wannan muhawara kuma bai kamata mutum ya dauki lamarin a matsayin wani abu da ake sukar shi kansa ba.
‘’Dole ne ka zama cewa a shirye kake ka fuskanci tambayoyi ka kuma yi fama da ra’ayoyin da suka saba da naka,’’ in ji ta.
‘’Kai ina ganin a gaskiya ma wannan wani abu ne da yake da muhimmanci ko ma in ce wajibi ga rayuwar mutum,’’ Ta ce.
‘’Eh gaskiya ne, wasu za su iya caccakarka, to amma kada wannan ya sa ka ji tsoronsu.’’
Asalin hoton, Stephanie Vilchez
‘’Dole ne ka zama cewa a shirye kake ka fuskanci tambayoyi ka kuma yi fama da ra’ayoyin da suka saba da naka,’’ in ji Fatou
Sai dai wannan ba wai yana nufin cewa al’amarin abu ne mai dadi ba fa, domin Fatou ta nuna cewa a wani lokacin takan kaurace wa karanta sakonni ko martani a kan wani abu da ta rubuta a shafukanta na intanet, abin da ta kira,’’kariya’’.
‘’Ina da kawaye da abokanai bakaken fata da dama wadanda ke rubuta abubuwa da dama a shafukan intanet, wadanda a yanzu sun rufe shafukan nasu saboda ba za su iya jure wa cin zarafi ba,’’
‘’Dole ne ka san yadda za ka dan iya kare kanka.’’
‘Duk wanda ya daina rubutu a shafin intanet saboda masu cin zarafi yaki ya ci shi’
Fatou ta ce samar da wata kafa ta wayar wa da mutane kai su samu kwarin guiwa na yakar kalaman cin zarafi muhimmin mataki ne na samun kwanciyar hankali, amma kuma ba ta ganin cewa mutum ya kawar da kansa kawai ya ce ba ruwansa a matsayin wata hanya ta kariya.
Masu cin zarafi suna son tashin hankali ne kuma galibi ana samunsa ta bangaren wariyar jinsi ko bambancin launin fata ko kuma tsabar jahilci a kan batun da suke sukan mutane a kai.
Amma fa kada a yi mun gurguwar fahimta, dole ne a dauki duk wani laifi da muhimmanci, to amma mummunan martani ya fi nuna irin mutanen da ke suka na fiye da abin da nake rubutawa,” in ji Fatou.
Mai fafutukar ta jaddada muhimmancin mutum ya kasance mai juriya kan duk wani suka ko cin zarafi da za a yi masa, kuma kada ya bari abin ya sa ya bar shafin sada zumunta da muhawara.
‘’Duk mutumin da ya kaurace wa shafin sada zumunta ya daina rubuta wani abu saboda masu cin zarafi hakan na nufin ya bayar da kai ke nan an ci shi da yaki na wariyar launin fata.
‘’Idan muka daina magana a kan muhimman abubuwa to wannan shi ne abin da masu kyama ke so ke nan,’’ in ji Fatou.
Damarmaki da barazanar da ke shafukan sada zumunta da muhawara
Fatou tana da kwarin guiwa a kan tasiri da muhimmancin mutane su tashi tsaye wajen fafutuka tare da jan jama’a a wannan fafutuka.
Ta nuna cewa ta iya samun goyon baya daga jama’a bayan abin da ya faru da ita na cin zarafi na wariyar launin fata a 2020 a shafukan sada zumunta da muhawara tun ma kafin labarin ya bulla a kafafen yada labarai.
Ta nuna cewa a kullum kafafen intanet na kara samun muhimmanci a rayuwarmu, inda za mu iya amfani da su wajen fadakarwa a kan wariyar launin fata da hakkin dan’Adam da kuma bayyana wa duniya irin halin da mutum ya samu kansa a ciki ba lalle sai ta wata kafar yada labarai ba.
Ta ce, “kamar ni a kana bin da ya faru da ni, misali ta hanyata mutane sun san irin halin da matashiya bakar fata kuma ‘yar ‘yan ci-ranin Afirka a Brazil ke ciki.’’
To amma kuma Fatou ta yi gargadin kada mutum ya bari harkar shafukan sada zumunta da muhawara ta mamaye shi.
Ta tuna yadda wannan abu da ya faru da ita ya sa ta yi suna a lokacin take shekara 15 da haihuwa, kuma ta yadda cewa lalle hakan ya dauki hankalinta sosai.
‘’Ina ‘yar yarinyata kawai sai kawai na samu kaina a yanayi na yadda mutane ke ta zargina da yin watsi ko kawar da kai a kan wani batu ko mutum. Akwai fa dawainiyar karatu a gabana,’’ kamar yadda ta fada tana dariya.
‘’A wurina sanya abu a shafin intanet abu ne da kake so ba wai abin da ya zama dole ka yi ba.’’
“Ba wani nauyi da ya rataya a wuyanka na wadannan mutane.”