Yajin aiki ya durkusar ya tsayar da al’amura cak a jami’o’in Najeriya


wp-1478696918739.jpg

 

Rahotanni na cewa, an dakatar da bayar da darussa a jami’oin Najeriya sakamkon yajin aikin gargadi na mako guda da kungiyar ta fara.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar dattawan Najeriya sun bukaci shugaban Majalisar Bukola Saraki da ya shiga tsakanin gwamnatin Tarayya da malaman jami’o’in.

Kungiyar malaman dai ta fara yajin aikin na gargadi inda ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta cika mata alkawarurrukan da ta yi kuma suka amince a kai a shekarun da suka gabata.

You may also like