Yan ƙasar Ghana 127 sun dawo gida daga Libya 


Yan ƙasar Ghana yan ci rani 127 ne suka dawo gida daga ƙasar Libya ta hanyar taimakon gwamnatin ƙasar wacce tace tana yin ƙoƙarin ganin ta kwaso dukkanin yan ƙasar da suka makale a ƙasar Libya zuwa gida.

A cewar daya daga cikin mutanen da suka dawo gida akwai yan ƙasar ta Ghana sama da mutane  170 dake wuraren da ake tsare mutane a ƙasar Libya.

Ministar Harakokin Wajen Kasar, Shirley Ayittey, wacce ta jaddada kokarin gwamnati na kula da walwalar yan kasar mazauna kasar waje, ta fada a karshen mako cewa ana ci-gaba da kokari don ganin an kubutar da dukkanin yan kasarta dake tsare a ƙasar Libya.
Labarin da ke cewa ana sayar da bakar fata yan Afirka a matsayin bayi a ƙasar ta Libya ya jefa zukatan gwamnati dama yan kasar ta Ghana cikin fargaba hakan yasa gwamnati ta shiga neman hanyar da zata dawo da yan kasarta gida.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like