Dubban jama’a magoya bayan ‘yan adawa a Gabon sun gudanar da wani gangami tare da yin marchi domin nuna alhini ga jama’ar da suka rasa rayukansu.
A sakamakon tashin hankali da ya faru biyo bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da hukumar zabe ta yi a makon jiya wanda Ali Omar Bango ya lashe.
Jagoran ‘yan adawar Jean Ping wanda ya jagoranci marchi tare da rakiyyar wasu ‘yan adawar,ya jawabi a gaban wani dandali da aka yi marchin domin tunawa da wadanda suka mutu.Mutane akalla guda biyar suka rasa rayukansu a kasar ta Gabon a sakamakon tashin hankalin da ya barke bayan zaben shugaban kasar yayin da wasu da dama suka jikkata.