‘Yan Adawa A Gambiya Zasu Tsaida Dan Takara Guda


 

Jam’iyyun adawa a Gambiya sun amunce su fitar da dan takara guda a zaben shugaban kasar a watan Disamba mai zuwa.

A wata sanarwa da suka fitar a Banjul a ranar Juma’a data gabata ‘yan adawan sun ce zasu kauda banbance banbance dake tsakaninsu domin tsaida dan takara guda da zai fafata da shugaban kasar mai barin gado Yahya Jammeh a zaben mai zuwa na ranar daya ga watan Disamba na wannan shekara.

Kawo yanzu dai ‘yan adawa basu bayyana suna dan takara da zai tsaya masu a zaben ba.

A watan fabrairu daya gabata ne jam’iyya mai mulki a kasar APRC ta tsaida mista Jammeh dan shekaru 51 daya kwashe shekaru 22 yana shugabancin wannan karama kasa dake yammacin Afrika a mastayin dan takara a zaben mai zuwa.

Mista Jammet wanda ke neman wa’adin mulki na biyar ana zarginsa da kama karya batun da ya jima yana musuntawa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like