Yan adawa na zargin yunkurin magudi a zaben raba gardama a Cote D’Ivoire


 

A yau Lahadi yan kasar Cote D’ivoire za su bayyana ra’ayin su a zaben raba gardama dangane da batun kawo gyara ga kudin tsarin mulkin kasar kamar dai yadda Shugaban kasar Alassane Ouattara ya shigar da wannan bukata.

Ga duk alamu yan adawa sun bayyana damuwa tareda yi kira zuwa magoya bayan su na gani sun kada kuri’ar kin amincewa da haka.

Gwamnatin kasar ta dau matakan tsaro domin gujewa duk wani tashin hankali a wasu mayan biranen kasar da suka hada da Abidjan,Bouake,Yamoussokro.

Hukumar zabe ta bayyana cewa kusan mutane milliyan 6 da 300 ne suka samun yi rijista.

You may also like