‘Yan adawa za su hana a rantsar da Deby a Chadi


 

 

‘Yan adawa a kasar Chadi sun lashi takobin hana rantsar da Idirs Deby a matsayin shugaban kasar domin nuna rashin amincewa da galabar da ya samu inda za a rantsar da shi domin yin wa’adin mulki karo na biyar a ranar 8 ga wannan wata na Agusta a birnin Ndjamena.

Gamayyar kungiyar ‘Yan adawar ta FONAC ta shirya gudanar da gangamin ne a ranar da za a rantsar da shugaban.

‘Yan adawar sun ce za su yi maci a sassan birnin N’Djamena tun daga ranar Asabar har zuwa Litinin 8 ga watan Agusta da za a yi bikin rantsar da Idris Deby.

Shugaban ‘Yan adawar Saleh Kebzabo ya ce Deby haramtaccen shugaba ne a Chadi.

A watan Afrilu aka sake zaben Deby a wa’adin shugabanci na biyar inda ya samu kuri’u sama da kasha 60 yayin da Saleh ya samu sama da kashi 12.

Tun 1990 Idris Deby ke shugabanci a Chadi.

You may also like