
Asalin hoton, Getty Images
Zakarun gasar cin kofin duniya, Argentina sun isa filin jirgin sama na Buenos Aires inda dubban jama’a suka fito domin yi musu maraba.
Gwamnatin kasar ta ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu domin gudanar da bukukuwa.
Magoya bayan kasar sun yi jerin gwano a kan titunan kasar domin yi musu maraba.
Nan gaba a ranar Talata ne za a gudanar da babban biki.
Lionel Messi ne ya soma fitowa daga cikin jirgi kafin sauran ‘yan kwallon kasar.
Asalin hoton, Getty Images
An saka hoton Messi a bindin jirgin da ya dauko ‘yan wasan daga Qatar
Asalin hoton, Getty Images
‘Yan wasan sun fito a saman motar bus domin amsa gaisuwar ‘yan kasar
Asalin hoton, Getty Images