YAN BANGA SUN KASHE YARO DAN SHEKARA 13 A KANOAl’ummar jihar kano, sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kano Dr. Umar Ganduje da su soke aikin (Vigilante-group) a jihar baki daya. Saboda yadda suke kashe jama’a da cin zarafin su a haka siddan musamman inda abin ya yi kamari a yankin arewacin kasar nan. 

Tun bayan kashe wani yaro dan kimanin shekara 13 da wasu ‘yan vigilante suka yi a unguwar Gobirawa dake Kano. Kungiyoyi a fadin jihar da kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka fara kiraye-kiraye ga masu ruwa da tsaki da su haramta aikin wannan kungiya saboda cin zarafin jama’a da su ke yi.

Yaron da suna kashe, Yaro ne wanda bai mallaki hankalin sa ba, suna wasa da yayansa sai suka tafi masallaci tare bayan an gama sallah sai yaran ya saka takalmin yayan nasa sai wani tsoho ya ce yaran ya saci takalmin sai ya mika shi ga ‘yan Vigilante group.

 Bayan sun yi wa yaran dukan kawo wuka kirjin yaron da kafarsa sun tabu nan take aka kai shi asibiti bayan kwana biyu yaro yace ga garinku nan. 

Matashin mai suna Muhammad Sani, wanda ke unguwar Gobirawa, ya rasa ransa ne a lokacin da ‘yan Vigilante suka kama shi bisa zargin cewar shine yake satar takalma a masallaci.

Inda ake zargin sun yi amfani da karfi wajan lakadawa yaran duka daga bisani yace ga garinku nan. 

Wakilimu ya nziyarci gidan su marigayin, inda ya zanta da mahaifiyarsa ta kuma nuna alhininta, inda ta ce an halaka mata danta ba tare da aikata laifi b.

Yayin jin ta bakin shugaban Kato da gora, ya musanta kisan. 

Tuni dai jami’an tsaro suka cafke wadanda ake zargin da kisan.

Bincike ya nuna cewar ‘yan vigilante suna kashe mutane masu yawa a duk shekara a arewacin Nigeria, mafi yawan wanda suke kashewa yara ne kanana wanda idan abun ya ci gaba Za su iya haddasa fitina a cikin Al’umma.

Ya kamata gwamnati ta dauki matakin gaggawa.

You may also like