Yan bangar siyasa sun kai wa sanata Hunkuyi hari


Sulaiman Hunkuyi sanata mai wakiltar mazabar arewacin Kaduna ya tsallake rijiya da bayan wani hari da yan bangar siyasa suka kai wajen taron masu ruwa da tsaki a jam’iyar APC ta jihar Kaduna.

Ya yin taron Hunkuyi ya yi kira ga magoya bayansa da su bijirewa duk wani shiri na kakaba musu yan takara a zaben shugabannin jam’iyar APC a matakin mazabu da aka shirya yi ranar 5 ga watan Mayu.

Ana tsaka da gudanar da taron ne, a otal din ENDwell sai yan bangar siyasa suka mamaye wurin dauke da muggan makamai iri-iri suna fadin “Sai Uba Sani, Sai El-rufa’i” tare da jefa duwatsu kan mahalarta taron.

Wadanda suka jikkata a harin an kai su Asibitin Barau Dikko da kuma Asibitin Garkuwa dukkanninsu dake cikin birnin Kaduna.

Motoci da dama maharan suka lalata ya yin kai harin.

Jame Obute, mai taimakawa sanatan kan harkokin yada labarai ya shedawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa an lalata motar, Tijjani Ramalan, shugaban jam’iyyar tsagin Hunkuyi.

Jam’iyar APC ta dade tana fama da rikici a jihar ta Kaduna har ta kai ga gwamnatin jihar ta rushe wani gini mallakin sanata Hunkuyi da tsagin nasa ke amfani da shi a matsayin Ofishi.

You may also like