
Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta ziyarci Villareal, domin buga wasan mako na 21 a gasar La Liga ranar Lahadi.
Barcelona tana matakin farko a teburin La Liga da tazarar maki takwas, tsakaninta da Real Madrid ta biyu.
Ita kuwa Villareal tana mataki na takwas a kan teburi babbar gasar tamaula ta Sifaniya da maki 31.
Kungiyoyin sun kara cikin watan Oktoban 2022, inda Barcelona ta ci 3-0 a Nou Camp.
Barcelona ta ci kwallayen ta hannun Robert Lewandowski, wanda ya zura biyu a raga daga baya Anssu Fati ya kara ya uku.
Idan Barcelona ta ci Villareal za ta bai wa Real, wadda ta lashe Fifa Club World Cup ranar Asabar a Morocco tazarar maki 11.
‘Yan wasan Barca da suka ziyarci Villareal:
Ter Stegen, R. Araujo, Gavi, Pedri, Lewandowski, Ansu Fati, Ferran, Iñaki Peña, Christensen, Marcos A., Jordi Alba, Kessie
Sauran sun hada da S. Roberto, F. De Jong, Raphinha, Kounde, Eric, Balde, Pablo Torre, Arnau Tenas da kuma A. Alarcón.