
Asalin hoton, Getty Images
Barcelona za ta karbi bakuncin Manchester United ranar Laraba a Nou Camp a wasan cike gurbin shiga ‘yan 16 a Europa League.
Barcelona ta koma buga Europa League a bana, bayan da ta kasa taka rawar gani a Champions League.
Wasa na 14 da za su kara a tsakaninsu, inda Barca ta ci shida da canjaras hudu, United ta yi nasara a uku.
Sun hadu sau biyu a Champions League a 2018/19, inda Barcelona ta doke United gida da waje, wato 1-0 a Old Trafford da 3-0 a Nou Camp duk cikin Afirilun 2019.
Shine wasa na karshe da suka fuskanci juna a tsakaninsu na 13.
Kungiyar Camp Nou tana ta daya a teburin La Liga da tazarar maki 11 tsakaninta da Real Madrid ta biyu.
United kuwa wadda ke fatan kammala Premier ta kakar nan cikin ‘yan hudun farko tana ta uku a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.
Tuni dai Barcelona ta bayyana ‘yan wasan da za ta kara da United:
‘Yan wasan sun hada da Ter Stegen, Araujo, Pedri, Lewandowski, Ansu Fati, Ferran, Christensen, Marcos Alonso, Kessie, S. Roberto da kuma Jordi Alba.
Sauran sun hada da De Jong, Raphinha, Kounde, Eric, Iñaki Peña, Balde, M. Casadó, Gavi, Pablo Torre, Arnau Tenas da kuma A. Alarcón.