‘Yan Bautar Kasa Sunyi Hatsari Sun Mutu A Hanyarsu Ta Komawa Gida Daga HoraswaInna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un!!! 
Cike da jimami muke sanar da labarin rasuwar masu yiwa kasa hidima su uku da suka rasa rayukan su a yayin hanyar su ta dawowa gida daga jihar Zamfara. Hadarin mota ne ya ritsa da su tsakanin garin Garo zuwa Gadon Kaya a jihar Kano. 

Daga cikin wadanda suka rasu akwai Limamin da ke Wa’azi jim kadan bayan idar da Sallah a Masallacin da ke sansanin horas da ‘yan gudun hijira na Tsafe. Kwana daya kafin rasuwar su ya yi Wa’azi cikin harshen Hausa. 

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya jikansu Ya gafarta musu. Ya wanke kura-kuransu Ya sa Aljannar Firdausi ce makoma.

You may also like