Wakilin Muryar Anurka a jihar Nija Mustapha Nasiru Batsari ya tattauna da wani Mazaunin Garin kuimo ta karamar Hukumar Mariga a jihar ta Nija, wanda yace tun a karshen makon da ya gabata suke cikin yanayi na tashin hankali domin kuwa ko a lokacin da suke magana da shi suna kan tsauni asakamakon musayar wuta da a ke yi a tsakain ‘yan bindigar da sojojin.
Agarin Adunu ma ta karamar Hukumar Paikoro A’immar garin ne ke cikin tashin hankali bayan samun labarin cewa ‘yan bindigar sun hallaka mutane 6 daga mutanen garin su kimanin 50 da suka yi garkuwa da su a makon jiya a cewar Alhaji Bakana, Sarkin Hausawam garin na Adunu.Kamar yadda Alh. Aminu Ibrahim Paiko shugaban Karamrt Hukimar ta Paikoro ya sanar da wakilin namu cewa hukumomin jihar Neja na kokarin daukar matakan shawo kan wannan matsalar.
Kawo lokacin hada wannan rahoto dai kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Nejan yaci tura. Haka zalika Gwamnatin jihar Nejan batayi wani karin Haske ba akan lamarin.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari cikin sauti: