Yan bindiga sun harbe ɗan sanda a Katsina


Kofural Ibrahim Surajo dake aiki da rundunar yan’sandan jihar Katsina ya rasa ransa bayan da wasu yan bindiga suka buɗe masa wuta kana suka yi awon gaba da bindigar sa.

Surajo tare da sauran abokan aikinsa suna aikin binciken ababan hawa a wani shingen bincike dake kan hanyar Kano zuwa Katsina da misalin karfe 8:30 na dare lokacin da lamarin yafaru.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar yan’sandan jihar,DSP Gambo Isa, yace yan bindigar sun zo ne a mota ƙirar Golf baƙa.

Ya ce Surajo yaje wani shago dake kusa da shingen binciken inda ya saka wayar salularsa caji lokacin da yan bindigar suka buɗe masa wuta kuma ya mutu nan take.

Ya ce rundunar ta samu wasu bayanai masu muhimmanci da za su taimaka wajen gano waɗanda suka aikata laifin.

You may also like