‘Yan Bindiga Sun Harbe Dan Bautar Kasa Har LahiraWasu ‘yan Bindiga da ake zargin’ yan fashi da makami ne sun harbe wani dan bautar kasa a b garin yenagoa dake jihar bayelsa, inda suka kwashe komai dake jikinsa wanda suka hada da kudade, salula, da dai sauran abubuwa. 
An tsinci gawar dan bautar kasar mai kimanin shekaru 30 da haihuwa a cikin bola inda bayan da aka kashe aka jefar dashi a wajen. 
Jami’in Hurda da jama’a na jamian yan sanda mista Asinim Butswat ya Tabbatar da faruwar wannan al’amari inda yace al’amarin ya faru ne a daren ranar asabar da ta gabata. 


Mista Butswat ya kara cewa, jami’an yan sanda suna nan suna ci gaba da bincike akan al’amarin. 

You may also like