A jiya Litinin, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wata mahakar zinare da ke jahar Zamfara in da suka hallaka akalla mutane 40, suka jikkata mutane da dama, yayin da wasu suka bata.
Duk da cewa ba’a tabbata ko su wanene ‘yan bindigar ba, ana kyautata zaton cewa ‘yan fashin shanu ne.
Al’amarin ya faru a mahakar zinare da ke daura da Kauyen Bindim da ke karamar hukumar Maru a jahar Zamfara.
Kafar yada Labarai ta BBC ta rahoto cewa yawancin wadanda suka rasu lebarori ne masu aikin hakar zinaren da kuma wasu ‘yan tsirare da suka zo saye.
Dama dai ‘yan bindiga sun shafe makonni suna matsawa mazauna yankin lamba da satar mutane suna neman kudin fansa.
Sai dai izuwa yanzu, hukuman tsaro ba su tabbatar da faruwar al’amarin ba.