Yan bindiga sun kai hari ofishin jakadancin  Faransa dake Burkina Faso


Wasu yan bindiga sun kai hari barikin sojoji da kuma ofishin jakadancin kasar Faransa dake Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Faso, a ranar Juma’a.

Wani sheda a wannan da abin ya yafaru ya ce yan bindiga fuskarsu a rufe dauke da  jakar goyo sun kai hari akan hedikwatar sojojin bayan fashewar wani abu mai kara da ake kyautata zaton bom ne.

Ofishin jakadancin ya tabbatar da faruwar harin cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Wani sheda ya fadawa kamfanin Dillancin Labarai na Rueters cewa an jiyo karar fashewar wasu abubuwa kanana a hedikwatar bayan babbar karar da akaji tun da farko. Tuni jami’an tsaro suka tattaru a wurin da lamarin ya faru.

Burkina Faso kamar sauran kasashen dake yankin Sahel na fuskantar hare-hare daga kungiyoyi yan ta’adda  dake yankin 

You may also like