‘Yan Bindiga Sun Kashe Akalla Mutane 50 A Kauyukan Jihar BenueRuben Bako, shugaban karamar hukumar Otukpo inda aka kai harin, ya ce ‘yan bindiga sun kashe mutane 47 a ranar Laraba a kauyen Umogidi da ke jihar Benue. Kwana daya kafin nan kuma aka kashe wasu mutane uku a kauyen, a cewar kamfanin dillancin labaran Associated Press.

Nan take dai ba a san dalilin kai hare-haren ba, ko da yake hukumomi sun ce suna da yakinin hare-haren biyu na da alaka.

Kaduna, Nigeria, Afrilu 16, 2019.

Kaduna, Nigeria, Afrilu 16, 2019.

Duk da cewa babu wanda ya dauki alhakin kai harin, hukumomi sun ce ana zargin Fulani makiyayan yankin, wadanda suka yi arangama da manoma a baya a kan rikicin filaye a yankin arewa maso tsakiyar Najeriya.

Manoman sun zargi makiyaya, wadanda akasarinsu Fulani ne, da yin kiwo a gonakinsu tare da lalata musu amfanin gona. Su kuma makiyayan sun dage kan cewa filayen na kiwo ne, da a karon farko doka ta amince musu a shekarar 1965, shekaru biyar bayan da Najeriya ta samu ‘yancin kai, a cewar AP.

Côte d'ivoire

Côte d’ivoire

Jihar Benue, da ake yi wa lakabi da “Kwandon abinci na Najeriya” saboda yalwar amfanin gona, na daya daga cikin jihohin da aka dade ana rikici tsakanin manoma da makiyaya a fadin arewa maso yammacin Najeriya da tsakiyar kasar.

Yawan amfanin gona da ake samu a jihar ya ragu cikin ‘yan shekarun nan saboda irin rikice-rikicen da ake yawan samu, lamarin da ke kara shafar iyalai a yankin da yawancin mutane ke fama da talauci da yunwa.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like