‘Yan bindiga sun kashe dan sanda daya a jihar Niger a wani hari da suka kai kan ofishin yan sanda


Jibril Abubakar, wani dan sanda mai muƙamin sajan dake aiki da rundunar yan sandan jihar Niger ya rasa ransa kana aka dauke bindigarsa lokacin da wasu yan bindiga suka kai hari kan ofishin yan sanda na Kutigi dake karamar hukumar Lavun ta jihar, a ranar Alhamis.

Muhammad Abubakar, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar shine ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar rundunar dake jihar.

Ya ce yan bindigar sun farma ofishin yan sanda dake Kutigi da misalin karfe 3:50 na daren ranar Alhamis inda suka rika harbin kan me uwa da wabi, amma masu gadin dake aiki sun samu nasarar dakile harin.

Ya ce, Dibal Yakadi, kwamishinan yan sandan jihar ya kafa wani kwamiti mai mutane bakwai karkashin jagorancin, Abdullahi Tahir, domin su bincika lamarin da kuma lalubo wadanda suka aikata haka domin su fuskanci sharia.

Ya kara da cewa rundunar ta yi alkawarin ladan ₦500,000 ga duk wanda yake da bayani mai mahimmanci da zai kai ga kama mutane.

You may also like