Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hare hare a kauyuka a Zamfara inda suka kashe sama da mutane 100 tare sace wasu da kone konen gidaje.
Hare haren sun auku ne a kauyukan kananan hukumomin Maradun, Shinkafi da Maru wadanda suka hada da Sabon Gida, Da Zazzaka, Da Zango, Da Tubali, Da Tukullu, Da Sububu, Da Kuma Dolen Moriki.
Ana ci gaba da ta’aziyar wadanda suka rasu yayin da ake lura da wadanda suka ji raunuka.
Wannan hare hare na zuwa ne dai bayan harin da aka kai wa leburorin da ke hako zinari a makon jiya a kauyen Bindin cikin karamar hukumar Maru inda aka kashe mutane kusan 40.
Duk da cewa rundunar sojin Nijeriya ta kaddamar ta Ofireshon Harbin Kunama a Zamfara, jahar na ci gaba da fuskantar matsalar tsaro da hare hare daga ‘yan bindiga.