Yan bindiga sun kashe mutane 10 a wasu k’auyuka dake jihar Kaduna


A kalla mutane 10 ne aka kashe a wasu hare-hare da aka kai a fadin jihar Kaduna.

Wata majiya ta shedawa jaridar The Cable cewa yan bindigar sun kashe mutane 8 ciki har da wani dagaci a garin Asso dake karamar hukumar Jema’a da kuma  kauyen Sarari dake karamar hukumar Birnin Gwarin ta jihar.

An ce harin da aka kai Asso an kai shine da misalin karfe 10 na dare.Mutanen da aka kashe na kan hanyarsu ta komawa gida bayan sun kai wani dan uwansu mara lafiya, asibiti dake Kafanchan.

Mutanen da ake zargi sun kai hari akan Sarari da karfe biyu na rana.Bayan sun mamaye kauyen, sun riƙa bi gida-gida suna harbe mutane.

Wani mazaunin yankin wanda ya tabbatar da faruwar harin  ya ce:” dauke suke da makamai kuma sun rika bi gida-gida suna harbin mutane, ” kowa na gudun neman tsira. An kashe dagacinmu da kuma wasu mutane biyar.

Nicholas Garba, dan majalisar wakilai ta tarayya dake wakiltar mutanen kananan hukumomin Jema’a /Sanga, wanda ya tabbatar da harin kan Asso inda yace karo na uku kenan ana kai hari kan al’ummar garin.

You may also like