Yan bindiga sun kashe mutane 30 a wani sabon hari da suka kai a jihar Zamfara


An rawaito yan bindiga sun kashe mutane 30 a wani sabon hari da suka kai jihar Zamfara.

A cewar jaridar Daily Trust harin ya faru ne ranar Asabar a kauyen Malikawa, dake gundumar Gidan Goga a karamar hukumar Maradun dake jihar.

Yan bindigar sun kashe mutane biyar da suke noma a gonarsu da kuma wasu mutane 25 da suka yi kokarin debo gawarwakinsu domin ayi musu jana’iza.

Mallam Makau, wani mazaunin yankin yace maharan sun ki yarda mazauna kauyen su yi jana’izar mutanen.Ya ce sun kai hari kan wadanda suka halarci jana’izar.

“Da sassaffe wasu magidanta biyar da suka tafi shuka iri a gonarsu, yan bindigar dake boye a wani daji dake makotaka da kauyen sun harbe su har lahira ,” Makau ya ce.

“Lokacin da mutanen yankin suka je debo gawarwakinsu yan bindigar sun shiga harbin kan me uwa da wabi inda suka kashe mutane 25.”

Muhammad Shehu, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce harin yafaru sakamakon rikici kan gonaki da bangarorin biyu suke yi.

You may also like