Yan bindiga sun kashe mutane uku a Plateau


Wasu yan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne sun kashe mutane uku a Dong dake karamar hukumar Jos ta arewa a jihar Plateau.

Terna Tyopev, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar shine  ya tabbatarwa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN  faruwar haka ranar Juma’a, a Jos.

A cewarsa mummunan lamarin da yafaru a daren ranar Alhamis ya bar wasu mutane da raunuka.

“Jiya da misalin karfe 7 na dare muka samu rahoton cewa wasu yan bindiga sun dirarwa al’ummar Dong  dake karamar hukumar Jos ta arewa inda suka kashe mutane uku, ” ya ce.

“Mun yi gaggawar tura jami’an tsaro ya zuwa yankin inda muka samu nasarar shawo kan lamarin.mun kuma a jiye wasu jami’an mu a garin domin kare faruwar wani harin da kuma karyewar doka da oda.”

Mai magana da yawun rundunar ya ce tuni aka binne mutanen da suka mutu ya kuma shawarci mazauna yankin da su kasance masu bin doka kana su kai rahoton duk wani abu da basu yadda da shi ba.

You may also like