Yan bindiga sun kashe mutane uku a  wanu ƙauye dake Numan


Yan bindiga a ranar Lahadi sun kashe aƙalla mutane uku a ƙaramar hukumar Numan  dake jihar Adamawa.

Mazauna kauyen Kikan sun fadawa jaridar Daily Trust a wayar tarho cewa gawarwaki uku aka gano na yan uwansu bayan wani hari da ake zargin Fulani makiyaya da kaiwa waɗanda suka dirarwa ƙauyen da misalin karfe 2:00 na dare,  suna harbi tare da kona gine-gine.

Rikici ya yi ƙamari a yankin tun bayan da aka kashe akalla Fulani mata da yara sama 55 a cikin watan Nuwamba da kuma harin da ya biyo baya kan wasu ƙauyuka da yawancin mazauna cikinsu yan kabilar Bachama ne inda aka kashe mutane da dama ya yin da kowanne bangare ke zargi juna  da laifi.

Sun ce maharan  da suka hawo kan babura sun iso ƙauyen lokacin da mutane ke bacci, suka shiga  cinnawa gidaje wuta tare da harbin mutane dake guduwa zuwa daji domin tsira da rayukansu, ya zuwa yanzu mutane uku aka tabbatar da sun mutu.

Da yake tabbatar da harin mai magana da yawun rundunar yan’sandan jihar Adamawa, SP Abubakar Usman , ya ce mutane biyu sun mutu wata mace ta jikkata yayin da aka kona gidaje da yawa lokacin da wasu yan bindiga suka kai hari ƙauyen.

You may also like