‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojojin Nijeriya Da Wasu A Yankin Naija Delta


Wasu ‘yan bindiga a garin Nembe da ke jihar Bayelsa da ake zargin tsagerun Neja Delta ne sun kashe sojojin Nijeriya uku da farar hula biyu a lokacin wani hari da suka kai musu a yau Litinin.

Lamarin ya faru ne a wurin binciken jami’an tsaron, yayin da suka kwashe makaman sojojin sannan suka tsere a cikin wani karamin jirgin ruwa.

Mataimakin Gwamnan  jihar Rear Admiral John Jonah kuma dan yankin garin na Nembe ya tabbatarwa manema labarai cewa, a yanzu haka an kara tura rundunar sojoji yankin don binciken lamarin.

You may also like